Home / Labarai / INA KIRA GA GWAMNA EL- RUFA’I YA KWATO MANI FILI NA – FIRDAUSI ABDULLAHI

INA KIRA GA GWAMNA EL- RUFA’I YA KWATO MANI FILI NA – FIRDAUSI ABDULLAHI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

AN yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, da ya Sanya baki domin kwato wa  Firdausi Abdullahi, filin ta.

Kiran ya fito ne daga bakin Firdausi Abdullahi, da ta kokawa manema labarai a cikin garin Kaduna, da nufin kai kukanta ga Gwamnan Jihar Kaduna domin a mayar mata da filin ta da take yin korafi a kai.

Wanda sanadiyyar hakan aka kai ta kotun Majistare ta 23 da ke zamanta a NDA Kaduna bisa zargin da ake yi mata cewa ta ba ta wa lauyan wanda take zargi da kwace mata fili, sanadiyyar hakan aka kai ta ajiya gidan Yari na tsawon kwanaki hudu.

“Ina da duk takardun fili da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce duk mai fili sai ya mallaka, don haka nake kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da ya kwato Mani fili na domin nawa ne ina da kowace irin takardar mallakar fili, ina kai kuka ga Gwamna ne domin ni ba ni da karfi”, inji Firdausi.

Firdausi Abdullahi, ta shaidawa manema labarai cewa ta dage a kan neman hakkin ta ne game da wannan filin domin goben yayan ta da ta haifa, in ba domin su ba, ba za ta dage a kan wannan fili na ta ba.

Da yake yi wa manema labarai karin haske Lauya A A Ashat, ya tabbatar wa da manema labaran cewa babu inda doka a cikin kundin tsarin mulki ta haramtawa dan kasa ya yi magana ko yin korafi ba.

“Amma kada ka taka kowa kada ka zagi kowa kada kuma ka musgunawa kowa, amma doka ba ta haramtawa dan Najeriya kada ya yi magana a kafafen yada labarai ba,saboda haka duk da haka mu a ra’ayin mu babu abin da ta fada da ya taka kowa ko ya ci mutuncin kowa ba don haka dadin abin shi ne  duk abin da ake magana a kansa magana ce da aka nadi bayanan kuma ya na nan Tangaran,saboda haka har yanzu muna jira don muga shi wannan abin da ake cewa ta fadi na musgunawa mu ji in har ya musgunawa wanda ake kara”, inji Lauya Ashat.

Lauya Ashat ya ci gaba da gayawa manema labarai cewa babu wani laifi idan Firdausi Abdullahi ta yi magana a kan maganar da take gaban kotu, amma abin da kotu take cewa kuma ko a wannan rana ma da aka shiga kotun shi ne in har kin yi maganganu na musgunawa, to, kada ki kara yi, tun da kotu korafi aka yi mata domin ba a kai gabar da za ta tabbatar da an yi maganganun ko ba a yi ba, saboda haka kotu ta yi mata Dabai bayi ta yi mata takunkumi cewa kada nan gaba in baki yi ba to nan gaba kada ki yi, in kuma kin yi to nan gaba kuma kada ki kara, saboda haka magana a kafafen yada labarai hakki ne wanda babu wanda zai dauke shi kuma kotu ba ta kwace mata wannan hakkin ba har yanzu. Iyaka ba ta da hurumi ko wani karfin da za ta yi magana da zai taka kowa ko wani ma’aikacin kotu ko abokin shari’a ko lauyan abokin shari’a wannan ya saba wa ka’ida.

A game da ko za su ci gaba da yin shari’a a wannan kotun kuwa?

Sai lauyan ya ci gaba da cewa a yanzu suna nan suna yin shawarwari domin matakin da nake shaida maku cewa za mu dauka na shari’a muna nan kuma nan da kwana biyu zuwa uku zaka samu amsar wannan tambayar, ta idan za mu ci gaba da shari’a a wannan kotun ko yaya lamarin zai kasance ko za mu ci gaba a wannan kotun ko za mu canza wuri duk zaku samu bayani, amma yanzu muna nan muna shawarwari na matakan da za mu dauka, amma fa na shari’a.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.