Home / Labarai / Ina Kulawa Da Marayu Sama Da Hamsin A Gidana – Rabi’u Musa

Ina Kulawa Da Marayu Sama Da Hamsin A Gidana – Rabi’u Musa

Mustapha Imrana Abdullahi
Muhammad Rabi’u Musa shugaban kungiyar Almuharram da ke zaman kanta domin taimakawa marayu da dukkan marasa galihu a yankin karamar hukumar Chikun ya bayyana irin nasarorin da ya samu da suka hada da Tallafawa matasa yin karatu da sauran fannonin rayuwa baki daya.
Muhammad Rabi’u Musa, ya ce kungiyar da yake yi wa shugabanci ta Almuharram na kokarin fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiyavtare da Juna ta yadda al’umma za su amfana har wasu da yawa su samu nasarar cin moriyarsu.
” A kokarin mu na tabbatar da zaman lafiya a yankin karamar hukumar Chikun muna shirya tarurrukan fadakarwa domin wayar da kan jama’a su san muhimmancin zama tare kuma mu na kokarin lalubo mutane mu kuma biya masu kudin rubuta jarabawar hukumar JAMB, ba tare da la’akari da irin addini ko kabilar da suka fito ba manufa dai shi ne a tabbatar an taimakawa yan Adam rayuwarsu ta inganta”, inji shugaban Almuharram.
Ya ci gaba da cewa su a matsayinsu na yan Jihar Kaduna su na goyon bayan kokarin da Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, yake yi na ganin an samar da yan Sandan Jihohi domin amfanin al’ummar kasa baki daya.
Ya kuma yi kira ga jama’ar Jihar Kaduna baki daya da su ci gaba da yin hakuri nan gaba kadan za a ga amfanin kokarin ciyar da Jihar Kaduna da Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i yake yi.
” Ni a gidana ina tare da yara marayu sama da 50 ina kula da su ta fuskar ilimi, lafiya, abin da za su ci da dukkan fannonin rayuwa ganin irin yadda jama’a ke cikin wani hali mawuyaci”.
Mohammad Rabi’u Musa ya ce su na kokarin koyawa jama’a dabarun yadda za su inganta rayuwarsu ta fannoni daban daban da suka hada da taimaka masu da abubuwan masarufi domin tafiyar da rayuwa, wanda hakan zai taimaka a samu zaman lafiya a tsakanin al’umma.
“Ko a lokacin wannan karamar Sallar da aka yi na Sanya an nemo mini yara marasa galihu da yawa na samo hayar abin wasan yara da suka hada da Lilo na wasan yara aka yi masu abinci mai kyau suka yi ta wasansu domin a samu saukin rayuwa kuma yaran da iyayensu su san cewa su na cikin al’ummar da ta damu da su matuka.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.