Home / Labarai / Tsarin Yan Sandan Jihohi Zai Rusa Dimokuradiyya – Tanko Yakasai

Tsarin Yan Sandan Jihohi Zai Rusa Dimokuradiyya – Tanko Yakasai

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani Dattijo daga arewacin Nijeriya Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana batun da wadansu mutane ke yi na samar da yan Sandan Jihohi matsayin tsarin da zai rusa Dimokuradiyya baki daya.
Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Tanko Yakasai ya ci gaba da bayanin cewa tun da farko ma ya dace jama’a su san cewa a Najieriya babu kudin da za a iya gudanar da tsarin yan Sandan Jihohi.
Ya bayar da misalin cewa ” a kananan hukumomi 774 da ake da su idan ana bukatar yin Yan Sandan jihohi a kalla sai an samar da mutane dubu dari uku (300,000) kuma abin da za a kashe masu na kudin kayan aiki,motoci,kayan sawa,takalma,ofisoshi da dai sauran kayan aiki dole sai an nemi kudi akalla yawan abin da ake kashewa Yan Sandan Gwamnatin tarayya wanda Nijeriya a halin yanzu ba irin wannan kudin.
Kuma ya ce akwai matsalar da za a iya samu ita ce wasu Gwamnonin za su iya yin amfani da Yan Sandan Jihohi su biya bukatunsu na kashin kansu, wanda hakan zai saba da irin abin da ake nufi na yin maganin matsalar tsaro

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.