Home / News / JAMA’A NE SUKA TSAYAR DA NI TAKARA – SIDI BAMALLI

JAMA’A NE SUKA TSAYAR DA NI TAKARA – SIDI BAMALLI

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Ibrahim Sidi Bamalli, dan takarar kujerar majalisar Dattawa ne a yankin shiyya ta daya a Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Lebo ya bayyana cewa yanci,Cancanta kuma da mutane ne suka ce sai ya tsaya wannan takarar domin shekaru sa sun kai abin da ake bukata saboda ya wuce shekaru Sittin koda yake ni yaro ne a wurin wasu mutanen.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

“Hakika kamar yadda na Sani cewa alkawari kaya ne don haka duk wanda ya dauka ya Sani cewa ya dace ya cika shi, babban alkawari dai a yanzu shi ne idan munje majalisa mu taimaka a kawo zaman lafiya domin hakan ne ya addabi mutane, sai harkar ilimi, dogaro da kai, a taimakawa mata da matasa ta yadda za a koma Noma mu fuskanci gaskiya kawai.

Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma cewa su Sani fa a yanzu ba aikin Gwamnati domin ya kare saboda ko shugaban kasa da kansa ya fadi hakan kuma muna gani a yanzu aikin mutane dari mutum daya da kwamfuta sai ya yi shi, saboda haka mu san cewa ba aikin Gwamnati sai aikin dogaro da kai”.

Kuma muna son mutane su Sani cewa duk dan majalisa akwai aikin da aka shata masa a dokar kasa ya yi saboda haka jama’a su kiyayi duk wani mai neman kujerar majalisa da zai ce masu zai kawo masu tituna domin wannan duk shaci fadi ne kawai, domin idan ma dan majalisa na son ya yi wani abu sai dai ya roki Gwamna, shugaban karamar hukuma ko Shugaban kasa ayi masa wani aiki kamar titi,gine gine da sauran wadansu makamntansu saboda haka idan Allah ya kai mu ga lashe zabe za mu haskakawa Gwamna, Shugaban kasa irin ayyukan da mutanen mu ke so wanda idan Allah ya yarda za a samu”.

Ibrahim Sidi Bamalli, ya kuma kara da ankarar da jama’a cewa kowa ya tabbatar katin zabensa na nan a kusa domin shi ne makamin da za a yi amfani da shi a ranar zabe domin samun nasara, musamman ga matasa Maza da Mata muna kara yin kira a gare su.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.