Home / News / Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kaduna Sun Dage Zabe Saboda Umarnin Kotu

Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kaduna Sun Dage Zabe Saboda Umarnin Kotu

 Imrana Abdullahi
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna sun bayar da sanarwar dage zaben shugabanninsu da za su jagoranci matakin Jiha sakamakon umarnin kotu da suka samu da ya yi masu hani da hakan.
 A cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun Honarabul Bashir Dutsinma da Honarabul Abdullahi Ali Kano shugaba da sakataren kwamitin rikon da uwar jam’iyyar ta aiko Jihar
 Takardar sanarwar ta ci gaba da cewa zaben shugabannin kananan hukumomi tuni aka kammala su a ranar 26 ga watan Agusta, 2020, kuma an yi cikin nasara.
Kuma shirye shiryen yin zaben shugabanni na jiha a ranar 29 ga watan Agusta, 2020 shirin ya yi nisa amma sai ga takardar kotu
 ” An kuma kawo mana takardar kotu a ranar 27 ga watan Agusta, 2020 da misalin karfe 4 na Yamma daga babbar kotun Jihar Kaduna.
 ” A matsayin mu na masu bin doka,  saboda haka zaben shugabannin jam’iyyar da aka ambata za a gudanar da shi a ranar Asabar 29 ga watan Agusta, 2020 domin zaben shugabannin Jiha a yanzu an dage shi za a sanar da wata sabuwar rana a nan gaba”, inji yan kwamitin riko

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.