Home / News / JAM’IYYAR PDP TA KADDAMAR DA KWAMITICIN KAMFEN NA SHUGABAN KASA DA GWAMNA A KADUNA

JAM’IYYAR PDP TA KADDAMAR DA KWAMITICIN KAMFEN NA SHUGABAN KASA DA GWAMNA A KADUNA

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna ta kaddamar da manya manyan kwamitocin  Yakin neman zaben Gwamna, shugaban kasa da kuma na masu bayar da shawara.
Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Mista Felix Hassan Hyet, lokacin da yake kaddamar da kwamitoci ya ce an samar da su ne domin samun nasara a kowa ne mataki da za a gudanar da zabe.
Mista Felix Hassan Hyet bayani ya yi cewa an yi wannan shirin ne domin samun kuri’un al’umma a Jihar Kaduna karkashin hadadden gamammen tsari shugabanci
Sai ya bayar da shawarar cewa samun nasarar jam’iyyar musamman a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Babban kwamitin Yakin neman zaben wanda ke karkashin jagorancin Malam Haruna Yunusa Sa’id Kajuru,
ya ce wannan kwamitin shike da ikon samar wa da shirya yadda za a yi Yakin meman Zaben da zai samar da nasara a matakin Jiha.
“Zamu tabbatar da cewa an gudanar da aiki domin samun nasarar dawo wa da PDP bisa madafun iko, saboda abin da muka Sani babbar jam’iyya a Jihar Kaduna a shirye take ta dawo da mulki inda aka san shi bayan lashe zaben yan majalisun jiha da na tarayya a zaben 2023”, inji Hyet.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban Yakin neman zaben Darakta Janar Mallam Haruna Saeed Kajuru, godiya ya yi wa PDP a game da yadda suka ga ya dace a bashi wannan matsayin sai ya ba su tabbacin yin aikin samun nasara PDP a Jihar Kaduna.
Mallam Haruna Sai’d Kajuru, kira ya yi ga daukacin al’umma da su hada kai domin ceto Jihar Kaduna daga halin da take ciki a yanzu
 Da yake nasa jawabin dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin PDP Mallam Isa Ashiru Kudan, godiya ya yi ga masu ruwa da tsaki da sauran shugabannin jam’iyya shawartar su ya yi da su yi aiki domin samun nasarar jam’iyyar.
Mallam Isa Ashiru Kudan ya tabbatarwa shugabanni da baki dayan yan kwamitin kamfen da aka kaddamar cewa zai ba su cikakken hadin kai da goyon baya domin a samu nasarar da kowa ke bukata.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.