Home / Labarai / Jihar Kaduna Abin Tausayi Ce – Mohammad Abubakar

Jihar Kaduna Abin Tausayi Ce – Mohammad Abubakar

Imrana Abdullahi
An bayyana Jihar Kaduna a matsayin Jihar da ta zama abin tausayi sakamakon irin halin tattalin arzikin kasa da aka shiga.
Tsohon Sakataren Ilimin karamar hukumar Kaduna ta Arewa Muhammad Abubakar ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Ya ce halin da tattalin arzikin da aka shiga irin kudin da Jihar ke samu daga Gwamnatin tarayya da kuma kudin shigar da ake samu a cikin gida duk abin ya yi kasa saboda matsalar cutar Korona da duniya ta shiga.
“Kudin mai ne da ake samu daga Gwamnatin tarayya a matsayin kudin kason wata wata da ake rabawa Jihohi, da kudin harajin cikin gida da ake tarawa duk abin ya yi kasa, don haka Jihar ta zama abin tausayi kwarai”.
A wani lokaci ma sai a rika duba Gwamnati ta ina za ta fara yin wadansu abubuwan da ya dace a aiwatar domin jama’a.
A matsayinsa na masanin harkokin ilimi tun a matakin karamar hukuma ya bayyana tsarin da Gwamnoni ke kokarin aiwatarwa mayar da masu karatun allo gidajensu da cewa akwai kuskure a ciki.
” Shin wani ko wasu yaran an san matsayinsa iyayen suna da rai ko ba su da rai, abin da ya dace shi ne Gwamnati ta aiwatar da kyakkyawan tsarin kula da daliban a sama masu da kayan karatu da wuri karatun da ingantattun malamai da yanayi mai kyau, amma ba kwashe daliban zuwa garuruwansu ba hakika wannan ba matakin da ya dace bane”.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.