Home / News / 2023: Cin Zaben APC Akwai Mushkila – Injiniya Kailani

2023: Cin Zaben APC Akwai Mushkila – Injiniya Kailani

Imrana Abdullahi
Wani Jigo a Jam’iyyar APC Injiniya Dakta Kailani Muhammad ya bayyana cewa in ba ayi gyara ba cin zaben jam’iyyar APC a shekarar 2023 akwai Muskila.
Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Inda ya ce hakika idan ana son APC ta ci zabe a shekarar 2023 dole sai an yi gyara in ba haka ba lamarin cin zabe ba zai yuwu ba.
A matsayina na dan jam’iyyar APC ya dace kowa ya Sani cewa akwai gyara kuma dole ne a aiwatar da shi.
A gefe daya kuma yayan APC da wakilinmu ya tattauna da su sun shaida masa cewa hakika akwai matsala saboda mulkin APC ba a yi da ainihin mutanen da suka wahala tun farko musamman kamar yadda yayan CPC na asali suke korafin cewa a matakai daban daban tun daga kananan hukumomi zuwa Jiha ba a ma san da suna cikin jam’iyyar APC ba balantana a saka su a cikin mulkin da ake yi a karkashin Buhari.

About andiya

Check Also

Sokoto Gov. appoints Ag. BoIR Chair, Zaki Tambuwal

    GOVERNOR Dr. Ahmad Aliyu of Sokoto state on Tuesday appointed Alhaji Abubakar Zaki …

Leave a Reply

Your email address will not be published.