Home / Ilimi / Jihar Zamfara Ce Matattara Almajirai – Gwamna Matawallen Maradun

Jihar Zamfara Ce Matattara Almajirai – Gwamna Matawallen Maradun

Imrana Abdullahi

A lokacin da wadansu Gwamnoni a tarayyar Nijeriya ke kokarin raba Jiharsu da batun almajiranci sai ga Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Mohammed Matawallen Maradun Maradun shelar kiran dukkan wanda aka kora daga inda sule da su zo Jihar Zamfara a ba su masaki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa Yusuf Idris Gusau, Darakta Janar game da harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a tare da harkokin sadarwa.

Yusuf Gusau, ya ce Gwamnan ya bude Jihar ne ga Almajirai lokacin da yake karbar bakuncin da yake karbar bakuncin wadansu Malamai guda biyu, Shaikh Abdullahi Dallah Dallah, Limamin masallacin Juma’a na Sambo Dan Ashafa, Gusau da Shaikh Bello Kanwa lokacin da suka zo yi masa gaisuwar Sallah a gidansa da ke Maradun.

“Gwamnan ya kuma bayyana rushe kwamitin da ya kafa domin mayar da Almajirai garuruwansu kuma ya some batun kwashe almajiran”.

” Daukar wannan matakin ya biyo bayan kyakkyawan nazari ne da aka yi kan batun karatun almajiri a Jihar wanda yana bukatar a inganta shi me kawai a cikin karatun zamani da nufin samun ilimi mai inganci na boko da Islam”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa ” Ya soke batun dauke almajiran ne domin ya ba su sukunin samun matsuwa da kuma rage tsangwama da ake yi wa tsarin karatun Almajirai na musulunci na koyo da koyarwa a cikin kasar nan”.

“Almajiran nan suna da damar samun ingantaccen ilimi a dukkan matakan gudanar da mulki na kasa, kuma Jihar Zamfara na ciki kuma Gwamnatin da nake yi wa shugabanci a shirye take ta kawo tsare tsaren da za su inganta harkar ilimi a fadin Jihar baki daya da zai samu karuwar ga kowa, amma ba a kwashe su ba a mayar da su inda suka fito, kuma muna bayar da shawara ga dukkan wadanda aka kwashe daga wasu jihohi su komo jihad Zamfara”, Inji Gwamna Matawallen Maradun.

Da suke gabatar da jawabansu daban daban Malaman sun yi godiya tare da Jinjina ga Gwamnan bisa matakin da ya dauka.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.