Home / Labarai / JIMLAR SUNAYEN YANKUNA GOMA SHA TARA (19) DA GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA AMINCE DA GYARAN TSARINSU

JIMLAR SUNAYEN YANKUNA GOMA SHA TARA (19) DA GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA AMINCE DA GYARAN TSARINSU

Daga Imrana Abdullahi
Hukumar Tsara Birane da Samar da Cigaba ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta sake zaiyana jimlan jerin sunayen yankuna goma sha tara (19) wadan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da gyaran tsarinsu.
Bayanin hakan ya fito ne daga Nuhu Garba Dan’ayamaka, MNIPR, mataimaki Darakta a bangaren yada labarai a hukumar KASUPDA
Hukumar ta KASUPDA, ta bayyana cewa amincewa da gyaran tsarin yankunan ya biyo bayan dubi ne da yin sassauci wanda Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ga jama’a da al’ummomi da sauran kungiyoyi da suka
shiga filayen Gwamnati tare da yin gine-gine, wanda za su fuskanci rushe-rushe, amma bisa karanci aka warware matsalar da kuma amincewa da gyara tsarin (regularisation).
Ga jerin sunayen yankunan da aka amince da su kamar haka:
NITR, Unguwan Rimi(TPO148), NAFDAC,
Narayi(TPO1180), Chanchangi, Sabon Tasha(TPO1179), Oil Village, Mahuta(TPO1172), Danbushiya,
Millennium City(TPO1173), Sabon Gida, Millennium City(TPO1171), Gidan Daji, Millennium City(TPO1170), Danhonu1, Millennium City(TPO1209).
Sauran su ne: Unguwan Maigero1, Kamazou(TPO1206), Stello, Sabon Tasha(TPO1198), NITEL,
Television(TPO1199), Babban Saura, Kamazou(TPO1202), Chanchangi, Kinkinau(TPO1204), Maigero 2,
Kamazou(TPO1263), Buwaya, Gonin Gora(TPO1210), Gbagyi Villa(TPO1274), Tsohon Kamazou(TPO1271), Kamazou(TPO1272), da kuma Sterling, Mando(TPO1215).
Dan haka ana kira ga wadan da abin ya shafa da su nuna halin karanci ta wajan zuwa su nemi izinin gine-ginen su kamar yadda aka tanadar.
Sa’annan wadan da suka fara neman izinin, amma aka ummarcesu da su biya kudaden da aka sanya musu ko kawo wasu takardu ko zane da ake bukata domin cika sharudan samun izini, to amma ba su yi
hakan ba, ana bukatar su bi ummarnin.
A sani cewa: Hukumar ta dauki matatai domin samun izini cikin sauki ba tare da daukan lokaci ba, ta yadda za’a iya samu cikin makonni biyu -uku(2-3), sa’annan da yin rangwame a kan kudade da aka sanya
ta yadda za’a iya biya.
Dan haka, Hukumar ta bayyana kudirinta na daukar mataki da ya dace a kan wadan da suka ki bin wannan ummarni kamar yadda Doka ta tanadar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.