Home / News / Kadade Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Matasan PDP Na Kasa – ASMEFO

Kadade Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Matasan PDP Na Kasa – ASMEFO

Hadaddiyar kungiyar ‘yan Arewa masu amfani da sabbin kafafen yada zumunta don yada angizon jam’iyyar PDP a Arewa, wato Arewa Social Media Forum for PDP ta bayyana goyon bayanta ga takarar Hon. Muhd Kadade Suleiman a matsayin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa.
Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Yusuf Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna. Yusuf Abubakar ya bayyana cewar dukkan shugabannin kungiyar na jihohi goma sha tara har da kuma Abuja sun amince domin mara baya ga takarar Hon. Muhd Kadade Suleiman a matsayin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa.
Muhd Kadade Suleiman mai kimanin shekaru 25 da haihuwa, yana neman kujerar shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa baki daya a zaben da za ai a sati mai zuwa. Tuni dai uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta ware wannan kujera ga shiyyar Arewa maso yamma inda kujerar ta fada jihar Kaduna, inda nan ce jihar Muhd Kadade Suleiman.
“A halin da muke ciki kida ya canza, don haka dole rawa ma ta canza. Tunda batu ake na matasa, to ya zama dole mu goyi bayan matashi domin samun kaiwa zuwa ga nasara, don kuwa kowa ya san dan shekaru 25 shi ne cikakken matashi”
“Wannan ce ta sanya muke kira ga mambobin kungiyar ASMEFO a duk inda suke da su nuna goyon baya ga takarar Kadade Suleiman a matsayin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa” a cewar Yusuf Abubakar shugaban kungiyar ASMEFO na kasa.
Alhaji Yusuf Abubakar yana wannan jawabi ne a sakatariyar kungiyar dake Kaduna, inda ka kara da cewar “mun yi duba na tsanaki, munga cewar Muhammad Kadade Suleiman shi ne matashin da yafi dacewa domin ya jagoranci matasa domin basu dama suma a dama da su wajen tafiyar da harkokin siyasar kasarnan.”
“A halin da muke ciki galibin magoya bayan Jam’iyyar PDP matasa ne zalla, don haka, wannan ba karamar nasara bace ace an samu matashi irinsu domin ya rike wannan kujera ta shugaban matasa na kasa.”
“A baya mun san yadda ake samun mutane masu fiye da shekaru sittin suna rike wannan kujera, don haka yanzu an samu sauyi, don haka dole mu goyi bayan matashi domin kaiwa ga nasara.” A cewar Yusuf Abubakar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.