Home / Labarai / Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Allah-wadai Da kashe Shugaban Fulani Da Yara A Zariya

Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Allah-wadai Da kashe Shugaban Fulani Da Yara A Zariya

Daga Imrana Abdullahi

Kakakin majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya  Honarabul DaftaTajudeen Abbas, ya yi Allah-wadai da kisan wani bafulatani, Alhaji Shuaibu Mohammad da ‘ya’yansa hudu da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka yi a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa mai dauke da Sa hannu Musa Abdullahi Krishi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga kakakin majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya.

Alhaji Shuaibu Mohammad, shi ne Ardon Birni da Kewaye na Masarautar Zazzau.

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kashe shi tare da ‘ya’yansa hudu, wadanda kuma suka sace masa shanu 100, a daren ranar Asabar da ta gabata.

Kakakin majalisar Abbas ya bayyana kisan a matsayin mafi girman abin bakin ciki, dabbanci da ban tausayi, da kowa ya dace ya yi Tir da shi.

Shugaban majalisar ya yi kira ga dukkanin hukumomin tsaro a Jihar Kaduna da su kara kaimi wajen ganin an gurfanar da wadanda suka kashe shugaban Fulanin da ‘ya’yansa.

Shi ma shugaban majalisar Abbas ya yi kira da a kwantar da hankula yayin da hukumomin tsaro ke gudanar da aikinsu.

Ya mika sakon ta’aziyya ga Masarautar Zazzau, da iyalan marigayi Ardo, jama’a da gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan mummunan lamari da bashi da dadin ji.

Kakakin majalisar Abbas ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu, ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa iyalan hakurin jure rashin da aka yi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.