KALANDAR MUSULUNCI: GOBE LARABA HUTU NE A JIHAR KANO, OYO DA JIGAW
Daga Imrana Abdullahi, Kaduna
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta ayyana gobe Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar aiki – kyauta domin murnar shiga sabuwar shekara ta Musulunci ta 1445.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye a madadin gwamna Abba Kabir Yusif.
Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasa tattalin arzikin jiharmu da kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabinmu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.