Home / Kasuwanci / Kamfanin Dangote Ya Bunkasa Irin  Kudaden Kasashen Waje Da Najeriya  Ke Samu 

Kamfanin Dangote Ya Bunkasa Irin  Kudaden Kasashen Waje Da Najeriya  Ke Samu 

…Ta hanyar kayayyakin sa na da ake samarwa a cikin  Nijeriya

An bayyana Rukunin kamfanonin Dangote a matsayin daya daga cikin manyan masu samun kudin musanya na kasashen waje a Najeriya wanda hakan ke ba da gudummawa ga ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasar.

Da take jawabi a wajen bikin ranar musamman ta rukunin da kamfanin Dangote ya gudanar a wajen bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa karo na 18 a Abuja (AITF), Darakta-Janar na kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI), Misis Victoria Akai, ta ce kamfanonin Dangote sun taimaka wajen bunkasa.  yawan kudaden da ake samu daga kasashen waje ta hanyar fitar da kayayyakinsa, kamar Takin zamani, zuwa wasu kasashe.

“Bikin baje kolin kasuwanci na bana ya duba batun kayayyakin da ake yi a Nijeriya, kuma muna alfahari da cewa rukunin Kamfanonin Dangote shi ne zakaran gwajin dafi a cikin kayayyakin da ake yi a Najeriya,” in ji ta.

Ta yaba wa rukunin kamfanonin na Dangote bisa daukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci karo na 18, wanda ke da taken: “Kudi mai dorewa da Haraji a matsayin jagoran Tattalin Arziki.”

Da yake jawabi, Babban Darakta, Hulda tsakanin Gwamnati da Masu ruwa da tsaki na Rukunin Dangote, Injiniya Mansur Ahmed, ya ce kamfanin ya himmatu wajen bunkasa masana’antu a Afirka.

Yayin da yake lura da cewa Rukunin Dangote shi ne babban kamfanin da ke taimakawa bunkasar tattalin arziki, musamman kasancewar kamfanin a matsayin wanda ya fi samawa jama’a aikin yi, ya ce Shugaban Kamfanin Aliko Dangote yana da sha’awar yin ayyukan taimakawa ga daukacin al’umma da nufin samun ciyar da al’umma da kas gaba.

Mista Ahmed ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan kokarin kawo sauyi, da kuma matakai da dama da aka dauka na kara habbaka tattalin arziki.

A cewar Mista Ahmed hadin gwiwar da ACCI ya baiwa kamfanin damar baje kolin kayayyakin da kamfanin ya kirkira da dama tare da ba da gudummawar kason sa ga tattalin arzikin Najeriya ta hanyar baje kolin kasuwanci da kuma har zuwa kasashen Ketare.

Wannan takarda na iya ba da rahoton cewa rumfar kamfanin ta zama wurin da mahalarta kasuwar ke taruwa don hango samfuran sabbin abubuwa da aka nuna.

Sanarwar da Sashen Samar da Sakon Sadarwa na Kamfanin ya fitar ta ce an kafa teburi na musamman a rumfar kamfanin domin amsa tambayoyi yayin da ta bukaci mahalarta taron da su yi amfani da dimbin kayayyakin da suka hada da: Takin Dangote, Sugar kamfanin Dangote, Sumuntin Dangote. Gishirin Dangote da dai sauransu kayayyakin da kamfanin ya samar.

Baje kolin Kasuwanci zai gudana tsakanin Satumba 28 da Oktoba 9, 2023.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.