Home / Ilimi / Sanata Barau Jibrin Ya Baiwa Dalibai 870 Tallafin Karatu

Sanata Barau Jibrin Ya Baiwa Dalibai 870 Tallafin Karatu

Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu daga Jihar Kano na cewa kimanin dalibai dari 870 ne mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ya baiwa tallafin karatu.

Shirin bayar da tallafin karatu, ga dalibai 870 na Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano (YUMSUK).  shi ne kashi na biyu na shirin tallafin karatun da Sanata Barau Jibrin ya bayar.

Daliban, wadanda aka zabo daga mazabar Kano ta Arewa, inda dan majalisar yake wakilta, an ba su Naira dubu 20,000 kowannensu.

Da yake jawabi yayin rabon kyaututtukan a harabar jami’ar, shugaban ma’aikatan mataimakin shugaban majalisar dattawan, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce Barau ya kirkiro shirin ne domin tallafa wa daliban mazabarsa.

Sanarwa daga ofishin yada labarai na Sanata Barau ta ce an fara shirin bayar da tallafin ne a watan Agusta da dalibai 628 na Jami’ar Bayero Kano (BUK).

“Kowane daya daga cikin daliban zai samu kyautar Naira dubu 20,000 daga hannun Sanata Barau kuma duk dalibin Kano ta Arewa da ke karatu a Najeriya zai ci gajiyar wannan shirin.  Mun fara ne a watan Agusta tare da daliban BUK, kuma yau muna YUMSUK kashi na biyu,” inji shi.

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan damar su yi karatun ta nutsu domin su yi fice a harkar ilimi.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Ummussalam Haruna Yusuf, daliba mai matakin 300, ta godewa mataimakin shugaban majalisar dattawa bisa wannan karimcin.

“Babban kalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne harkokin sufuri da abincin da za mu ci yayin da muke makaranta.  Wannan karimcin da Sanatanmu ya yi zai taimaka mana a kan haka,” inji ta.

About andiya

Check Also

Relentless attempt to ridicule Ganduje futile, must stop — Group

  By; Our reporter A group under the auspice of Kano Concerned Forum has faulted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.