Home / Kasuwanci / Karancin Biredi Na Kara Yin Kamari A Zamfara

Karancin Biredi Na Kara Yin Kamari A Zamfara

Daga Imrana Abdullahi

Karancin biredi ya yi kamari a Jihar Zamfara yayin da gidajen biredi suka rufe saboda tashin farashin kayan masarufi.

Kungiyar masu sayar da biredi reshen jihar Zamfara, ta koka kan yadda hauhawar farashin fulawa da sauran abubuwan da ake bukata don samar da biredi ya tilastawa gidajen kayan abinci da yawa rufe a jihar.


Shugaban kungiyar na jiha Alhaji Yusuf Usman wanda shi ne sakataren shiyyar arewa maso yamma a wata hira da manema labarai a Gusau babban birnin jihar Zamfara ya bayyana haka.

Alhaji Yusuf Usman ya koka da yadda farashin kayan masarufi ya zarce abin da suke iya samu.

Ya kara da cewa, “Ba mu da wani zabi da ya wuce mu rage yawan abin da muke yi a fagen sana’ar ko kuma mu daina baki daya  ko kuma mu daina nomawa saboda yadda farashin kayayyakin ke ci gaba da hauhawa tun daga shekarar 2016”.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki domin a ci gaba da gudanar da harkokinsu kafin lamarin ya gyaru.

About andiya

Check Also

KASUPDA Organizes Stakeholders Engagement Programme

Community in the approved regularization layouts areas in Kaduna Metropolis have been advised to co- …

Leave a Reply

Your email address will not be published.