Home / Labarai / Karfe 12 Na Daren Gobe Kano Ba Shiga Ba Fita

Karfe 12 Na Daren Gobe Kano Ba Shiga Ba Fita

Imrana Abdullahi

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano Kwamared Abba Anwar ya bayyana cewa daga karfe sha biyun daren Gobe Juma’a Kano ba shiga ba fita domin za a rufe dukkan hanyoyin sama da kasa.
ABBA Anwar ya tabbatar da cewa babu wata tantama gobe idan lokacin ya yi duk wanda ya zo ko a Jirgin sama ya shiga filin Jirgin saman Kano sai dai ya tsaya a filin Jirgin amma ba zai shiga cikin garin Kano ba.
Anwar ya ci gaba da cewa ya bayyana hakan ne a kokarin Gwamnatin Jihar Kano na ganin ta dauki matakin da ya dace domin kaucewa yaduwar cutar Korona bairus.
Don haka ake sanar da Jama’a halin da ake ciki domin su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga dukkan tsare tsaren Gwamnati abisa niyyarta ta kubutar da Jama’a kada a shiga wani hali na daban.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.