Home / Lafiya / Karfe 12 Na Ranar Juma’a Zamu Ta Fi Yajin Aiki – Ma’aikatan Lafiya

Karfe 12 Na Ranar Juma’a Zamu Ta Fi Yajin Aiki – Ma’aikatan Lafiya

 

Imrana Abdullahi

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan kula da kiwon lafiya da aikin Jinya da Unguwar Zoma sun bayyana cewa da karfe 12 na ranar Juma’a mai zuwa za su shiga yajin aikin gargadi na sati daya a Jihar kaduna.
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da suka yi a Kaduna.
Inda suka cimma yarjejeniyar cewa sakamakon irin yadda Gwamnatin Jihar kaduna ke tafiyar da al’amuran ma’aikata a Jihar yasa suka yanke hukuncin tafiya yajin aikin gargadi na  kwanaki Bakwai.
Kwamared Dakta Steven Kache, Likita ne kuma shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya ne wanda ya shaidawa manema labarai cewa saboda irin yadda abubuwa suka kasa daidai ta ana cirewa ma’aikata Albashi duk da irin yanayin zaman gida da ake ciki, ha kuma su a matsayinsu na ma’aikatan kula da lafiyar jama’a sun samu mambobinsu har mutane 6 da suka kamu da cutar Korona bairus kuma ba a wurin killace masu cutar suke aiki ba suna aiki ne a asibitocin Jihar masu dauke da cutar suka kai masu ita har wurin aikinsu.
Dakta Kache, ya kuma ce ana cirewa mutane albashinsu watanni biyu kenan, amma kuma cire kudin baya nunawa a cikin takardun biyan albashin ma’aikata.
Saboda haka da wannan suke kiran Gwamnatin Jihar Kaduna da ta Sanya batun biyan kudin alawus alawus na masu kula da wadanda suka kamu da cutar Korona ya kasance a kowane asibiti ba sai a cibiyoyin kula da masu cutar kadai ba.
“Ana cire mana Albashi ba tare da amincewarmu ba, bamu ce kada a taimakawa wadanda suka kamu da Korona bairus amma ana cire mana Albashi babu wata yarjejeniya ko kadan daga bangaren ma’aikata wanda hakan ya sabawa ka’idar aikin kwadago na duniya”.
Kuma muna kira ga daukacin jama’a baki daya da duk wanda ya san zai sa baki a gyara wannan lamari to ya shigo cikin maganar kafin karfe 12 na ranar Juma’ar nan mai zuwa domin da sha biyun rana ta yi daidai zamu ta fi yajin aikin gargadi a ko’ina, Kafin mu tsunduma cikin na sai abin da hali ya yi a ranar biyar ga wata mai kamawa.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.