Home / Kasuwanci / KEDCO Shiyyar Kano Ta Yi Asarar Miliyan Dari 260 A Watanni Uku

KEDCO Shiyyar Kano Ta Yi Asarar Miliyan Dari 260 A Watanni Uku

 Imrana Abdullahi

 

Kamfanin  da ke kula rarraba wutar lantarki domin Sayarwa ga jama’a KEDCO shiyyar Kano,katsina da Jigawa sun yi kira ga daukacin al’umma su tashi tsaye wajen kulawa da layukan wura Tate da dukkan kayan da ake amfani da su wajen rabawa mutane da kamfanoni wutar lantarki.

Hukumar gudanarwar kamfanin ce ta yi wannan kiran sakamakon irin asarar da ta gani ta samu da kudin ya kai naira miliyan dari 260 a cikin watanni uku da suka gabata.

Sun tabbatar da cewa hakan ta faru ne saboda ayyukan batagari masu satar kayan da kuma wani lokaci su lalata su baki daya.
Kamar yadda hukumar gudanarwar kamfanin ta bayyana cewa sun samu rahotannin lalata transifoma da kuma lalata man da ake sanyawa transifomar kanta tare da sace kayayyaki da dama wanda hakan ya zamarwa kamfani da masu hulda da shi abin damuwa kwarai matuka.
 Sanarwar ta hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun Ibrahim Sani Shawai shugaban bangaren sadarwa da hulda da manema labarai na kamfanin shiyyar Kano ya ce suna kokari matuka domin ganin an sanarwa da masu hulda da su abin da ya dace ta hanyar kulawa da kaya samar da wadansu kayayyakin yin gyara a kan lokaci a duk inda ake bukatar haka a ko’ina da yake karkashinsu.
Amma takardar da Sani Shawai ya fitar ta bayyana cewa batagari masu lalata kayan nasu suna kawo masu cikas kwarai.
Wannan ne yasa a halin yanzu aka rasa samun wutar a wadansu wurare, saboda haka kamfanin ya ce ba za su ci gaba da amincewa da hakan ba. Saboda haka muke yin kira ga jama’a da su taimaka mana wajen Sanya idanu ga batagarin nan domin a kare dukkan kayayyakin KEDCO saboda hakan zai yi maganin masu kokarin lalata tattalin arzikin kasa.

Shawai, ya ci gaba da bayanin cewa muna yin kira ga jama’a ne saboda batagarin na yin amfani da yanayi ne su aikata aika aikarsu da ke yi wa tattalin arziki barazana, shi yasa muke kara fadakar da jama’a cewa su taimaka ta fuskar kare dukkan kayan da kuma bayar da rahoton duk wadanda ake zargin suna kokarin bata kayan ga jami’an tsaro.

“Muna yin gargadi ga dukkan masu aikata irin wannan aikin na lalata kayan kamfanin KEDCO suna lalata transifoma suna kwashe man da ke cikinta da su hanzarta baron aikata irin wannan aikin saboda kamfanin KEDCO ba za ta lamunci ci gaba da yi mata aika aika irin wannan ba, saboda duk wanda aka kama za a hukunta kamar yadda dokar kasa ta tanadar”. Inji Shawai.

About andiya

Check Also

Alleged budget padding : Northern NASS member shun rancour, disunity, to enhance developmental projects 

Kola Kano and Imrana Abdullahi NORTHERN members in the national assembly, have been called upon,not …

Leave a Reply

Your email address will not be published.