Home / Big News / Kotu Ta Bayar Da Malam Nasiru El- Rufa’i Beli

Kotu Ta Bayar Da Malam Nasiru El- Rufa’i Beli

 

Daga Imrana Abdullahi

Babbar Kotun Gwamnatin tarayya da ke zamanta a Unguwar NDA cikin garin Kaduna ta bayar da Belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i

Kamar dai yadda kotun ta ce ta bayar da Belin sa ne bisa wadansu sharudda.
Babban dan tsohon Gwamnan wanda ya kasance dan majalisar tarayya a halin yanzu mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa Honarabul Bello Nasiru El-Rufa’i ya shaidawa manema labarai irin farin ciki da jin dadin da suke da shi a wannan rana inda yake ta yi wa Allah hamdala da godiya bisa wannan Belin.
Wannan hoton Malam Nasiru kenan a lokacin da ya fito daga babbar kotu
Inda ya ce za su tabbatar an cika sharuddan Belin da aka gindaya masa domin Belin.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Yayin Da Aka Fara Jigilar Alhazai Daga Filin Jirgin Sama Na Gusau

  Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa sabon tarihi bayan da aka gudanar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.