Home / Labarai / Kotu Ta Ce Nasiru Yusuf Gawuna Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Kotu Ta Ce Nasiru Yusuf Gawuna Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Kotun sauraren kararrakinnzaben Gwamna a Jihar Kano tini ta Sallami Gwamna ABBA Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano, inda ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

An dai bayyana ABBA Kabiru Yusuf a matsayin Gwamna ne a karkashin jam’iyyar NNPP.

Kotun dai mai Alkalai guda uku ta ce hukumar zabe ta kwace shaidar satifiket na lashe zabe da ta ba ABBA Kabir Yusuf ta kuma bayar da ainihin shaidar lashe zaben ga Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.

Kotun dai ta rage yawan kuri’u dubu 165,673 saga cikin kuri’un Gwamna Yusuf da aka ce ba su da amfani saboda dukkan wadannan yawan kuri’un a jikin ainihin takardunsu da aka Jefa kuri’a duk ba su a Sanya masu hannu ba kafin Jefa kuri’ar don haka ba su da wani amfani kuma bai dace a kidaya su ba tun farko.

Zamu kawo maku bayanai nan gaba….

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.