Related Articles
Daga Bello Bashir, Abuja
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Mai Shari’a Peter Lifu ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta amince da kwamitin rikon kwarya ƙarƙashin Sanata Nenadi Usman a matsayin sahihin jagorancin Jam’iyyar Labour (LP).
A yayin yanke hukunci a ranar Laraba, Mai Shari’a Peter Lifu ya jingina da hukuncin Kotun Koli na ranar 4 ga Afrilu, 2025 wanda ya tabbatar da Sanata Usman, tsohuwar Ministar Kuɗi, a matsayin sahihiyar shugabar kwamitin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da taron gangamin ƙasa. Kotun ta umarci INEC da ta “gaggauta amincewa da kwamitin rikon kwarya ƙarƙashin Nenadi Usman a matsayin hukuma ɗaya tilo da ke wakiltar Jam’iyyar Labour.”
Alkalin ya bayyana cewa shaidun da ke gaban kotu sun nuna wa’adin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa ya ƙare, inda ya yi watsi da hujjar Abure cewa rikicin ya shafi cikin gida na jam’iyya ne don haka ba zai iya zama abin shari’a ba.
A cewar kotu, kafa kwamitin rikon kwarya “tilas ne” bisa umarnin Kotun Koli.
Abure tun da farko ya shigar da ƙara a Babban Kotun Tarayya yana neman tabbatar da matsayinsa a matsayin shugaban jam’iyya bayan cire shi. Duk da cewa Babban Kotun Tarayya da Kotun Daukaka Ƙara sun amince da ikirarin Abure kuma suka umarci INEC ta amince da shi, daga baya Kotun Koli ta rushe waɗannan hukuncin.
A cikin hukuncin jagora da Mai Shari’a Inyang Okoro ya gabatar, kotun koli ta amince da ƙarar da Sanata Usman da sakataren kwamitin rikon kwarya, Hon Darlington Nwokocha, suka shigar, tare da yin watsi da ƙarar da Abure ya ƙara. Kotun Koli ta kuma yi gargaɗi ga jam’iyyun siyasa da su bi ƙa’idar kundin tsarin mulkinsu wajen naɗa shugabanni, tare da shawartar jami’an jam’iyya da wa’adinsu ya ƙare da su sauka daga mukami a lokacin da ya dace.
THESHIELD Garkuwa