Home / Big News / Ku Ba tsaro Fifiko, Gwamna Uba Sani Ya Bukaci Shugabannin kananan hukumomi

Ku Ba tsaro Fifiko, Gwamna Uba Sani Ya Bukaci Shugabannin kananan hukumomi

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani ta bukaci daukacin shugabannin kananan hukumomin jihar da su maida hankali kan harkokin tsaro da samar da yanayi mai kyau na saka hannun jari da cigaba a jihar.

Gwamna Uba Sani ya yi wannan kiran ne a wata ganawa ta musamman da shugabannin kananan hukumomi 23 da kansiloli, wanda aka gudanar a dakin taro na Umaru Musa Yar’adua da ke dandalin Murtala a Kaduna, a ranar Talata.

A Wata sanarwa da ke dauke da  sa hannun mai magana da yawun Gwamnan  Muhammad Lawal Shehu, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Uba Sani, da ake yi wa lakabi da Molash a ranar 17 ga Oktoba, 2023 ya ce

Gwamna Sani ya umurci shugabannin kananan hukumomin da su gudanar da tarukan tsaro a mako-mako ko kuma na wata-wata a majalisun su inda ya jaddada cewa yana da matukar muhimmanci a hada kai da shugabannin addini da na gargajiya domin inganta tattara bayanan sirri da yaki da matsalolin tsaro da suka kunno kai kamar satar mutane, fashi da makami da sauran su domin inganta al’amuran zamantakewa.

“Ina rokon ku da ku ba da goyon baya da yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro tare da samar musu da muhimman bayanan da ake bukata domin gudanar da ayyukansu.  Ina kuma gode muku da kuke  tare da gwamnatin jihar wajen daukar ma’aikata sama da dubu 7 na hukumar ‘yan banga ta jihar Kaduna,” inji Gwamna Sani.

Bugu da kari, Gwamna Sani ya ja hankalin taron kan illar da kaura zuwa birane ke haifarwa ga ci gaban karkara, ya kuma bukaci shugabannin kananan hukumomin da su hada kai da masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin.

Da yake la’akari da mahimmancin tattalin arzikin karkara, ya baiwa shugabannin kudurin gwamnatinsa na ganowa tare da magance matsalolin da manoma ke fuskanta domin bunkasa ci gaban karkara a wani bangare na shirinsa na kawo sauyi a karkara.

Dangane da batun hada-hadar kudi, Gwamna Sani ya jaddada cewa yawan mutanen da ba su da aiki da kuma marasa galihu a jihar abin damuwa ne.  Ya jaddada kudirinsa na magance wannan matsala ta hanyar sanya hannu kan umarnin zartarwarsa na farko kan hada-hadar kudi.

Da suke mayar da jawabi shugabannin kananan hukumomin tare da kansilolinsu duk sun yaba da kokarin Gwannan da yake aiki tukuru Dare da rana domin ganin Jihar ta samu ci gaba.

Sun kuma jaddada kudirinsu na yin dukkan abin da ya dace domin aiwatar da abubuwan da suka dace ta yadda za a samu ci gaban tsaro da tattalin arzikin Jihar baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.