Home / News / KU BANI KURI’UNKU IN YI MAGANIN YAN BA NI NA IYA – ISA ASHIRU

KU BANI KURI’UNKU IN YI MAGANIN YAN BA NI NA IYA – ISA ASHIRU

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An yi Kira ga daukacin masu zaben dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC da su bayar da kuri’unsu ga dan takara Isa Ashiru Kudan.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar bayani da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Yakubu lere, Daraktan wayar da kan jama’a na kwamitin neman zaben Isa Ashiru.
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana kansa a matsayin dan siyasa lamba daya da ya samu nasarar lashe zabe sau hudu daga cikin biyar da ya tsaya a rayuwarsa.
Da yake jawabin mayar da martani cewa ba zai iya lashe zabe ba, Isa Ashiru ya jawo hankalin masu zaben dan takarar cewa irin yadda ake ga ne karfin dan takara ya danganta ga yadda zai hada tawagar fafutukar neman zabensa da nufin samun nasara wanda kuma har an samu nasarar lashe zabe sau hudu daga cikin biyar.
Sakamakon hakan Isa Ashiru ya yi kira ga daukacin masu zaben dan takarar da su dawo daga Rakiyar yan ta fadi gasassa kawai su bashi kuri’a domin kayar da jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
“Da suka zo kan madafun iko sakamakon raba wa da goya wa a bayan Buhari? Honarabul Kudan ya ba masu zaben dan takarar cewa zai tabbatar ya kawo gagarumin ci gaba a Jihar Kaduna.
A game da batun zarginsa da ake yi cewa ya sayar da zaben da ya tsaya a shekarar 2019 da ya gabata, sai ya jawo hankalinsu da cewa ta yaya duk wani mutum mai hankali zai amince da irin wannan maganganu?
“Ai kujerar Gwamna ba abu ne mai farashin Sayarwa ba wanda hakan ne ya sa ya yi kokarin yin shari’a domin tabbatar da karbo nasarar da ya samu saboda haka ya yaya zan yi hakan idan da an yi abin da suke zarginsa”.
Mafi yawan masu zaben daga kananan hukumomi 22 duk sun bashi tabbacin za su bashi kuri’unsu, inda suka tuna masa cewa kokarin da ya yi wajen ganin sun ci gaba da zama shugabannin jam’iyya ba za su ta ba mancewa da shi ba.

About andiya

Check Also

An Yi Addi’oin Musamman  Domin Samun Zaman Lafiya A Katsina

 A ranar Litinin din  da ta gabata ne 1 ga watan Augusta shekara  ta 2022  …

Leave a Reply

Your email address will not be published.