Home / Uncategorized / Kudirin Doka  A Kan Fadakarwa Da Gyaran Hali Na Masu Shaye Shayen Miyagun Kwayoyi Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Kudirin Doka  A Kan Fadakarwa Da Gyaran Hali Na Masu Shaye Shayen Miyagun Kwayoyi Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Sai dai kamar yadda wanda ya gabatar da kudirin a gaban majalisar Dattawa ta kasa Sanata Rufa’I Sani Hanga ya bayyana cewa da yawan yan majalisa sun yi mahawara a kan kudirin ba tare da sanin yadda lamarin yake ba.

Sanata Hanga ya ce wadanda ke cewa a hade wannan batu da hukumar yaki da sha da Fataucin miyagun kwayoyi lallai rashin fahimta ne kawa.

Saboda kamar yadda Sanata Rufa’I Hanga ya ce aikin masu aiki a hukumar hana sha da Fataucin miyagun kwayoyi shi ne su kama su hukunta wanda aka kama su hana. Amma wannan kudirin shi ne wayarwa da jama’a kai a game da illolin abin kuma tun daga kananan yara har zuwa sama a wayar da kansu a kan illolin miyagun kwayoyi sannan kuma a samar da asibiti na musamman da idan an samu wanda matsalar ta kama a san yadda za a yi cikin hanzari. Saboda kamar yadda Sanata Sani Hanga ya ce a duk Nijeriya ba asibitin kamar irin wanda ake son ayi domin masu wannan matsalar ko kadan don haka idan an samar da irin wannan asibitin za a iya samun wurin da za a taimakawa masu matsalar har su warke a kuma ba su wani jari suje su kama sana’a.

” Da yawan Sanatoci ba su fahimta ba, ni kuma na yi ta kokarin a ba ni damar in tashi domin yin karin bayani amma lamarin ya ci tura. Duk da ga abu a rubuce ga kuma hujjar amma dai ji na kawai suka yi ba su fahimta ba sai kawai a rika cewa ai wannan sai a kaiwa hukumar masu yaki da miyagun kwayoyi kawai. Na yi na yi da mai shugabantar majalisa a lokacin ya bar ni in yi magana amma lamarin ya ci tura “.

Sanata Hanga ya ci gaba da cewa amma wanda ya fara fasa kwai a zaman majalisar shi ne Sanata Dahuwa saga Jihar Bauci da ya ce shi Likita ne don haka wannan kudirin bashi koda kakanni da hukumar hana sha da Fataucin miyagun kwayoyi don haka abin da kudirin ke nema ayi babu irinsa a Nijeriya kuma a duniya akwaisu kala – kala a kasashen duniya saboda haka yakamata ayi duba da idon basira a kan lamarin nan. Bayan nan akwai sanatoci da yawa da suka goyi bayan kudirin.

Sai kuma wani ma da ya yi wa Sanatoci wato yan siyasa da kalubale da ya ce ai yan siyasa ne ke sawa a sha kwayar don haka kalubale ne ko ga wa Oho!

About andiya

Check Also

GWAMNA LAWAL YA ƘADDAMAR DA AIKIN GINA TASHAR MOTA TA ZAMANI A GUSAU, YA SHA ALWASHIN SAMAR DA GURABEN AYYUKAN YI

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na samar da guraben ayyukan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.