Home / News / Kungiyar ALGON Reshen Jihar Katsina Ta Rubuta Takardar Koke Zuwa Ga Ministan Shari’a

Kungiyar ALGON Reshen Jihar Katsina Ta Rubuta Takardar Koke Zuwa Ga Ministan Shari’a

Kungiyar ALGON Reshen Jihar Katsina Ta Rubuta Takardar Koke Zuwa Ga Ministan Shari’
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa reshen Jihar Katsina (ALGON) ta rubuta wa babban mai shari’a kuma ministan shari’a babban lauyan Nijeriya Alhaji Abubakar Malami takardar Koke suna korafi a kan kin bin umarnin kotu da Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello ya yi na mayar da shugabannin kananan hukumomin da aka zaba tun kafin Gwamnan ya dare kan madafun ikon Jihar.
Takardar tasu na bayani ne kan irin yadda aka ki bin umarnin da kotun koli ta bayar ta hanyar yanke hukunci cewa a mayar da zababbun shugabannin kananan hukumomin da aka zaba amma aka cire su ba tare da bin doka ba musamman tanaje tanajen Dimokuradiyya duk da cewa an Zabe su ne ta hanyar tsari iron na zabe da dokar kasa ta amince da shi a matakan kananan hukumomi.
In dai za a iya tunawa Gwamna ya sauke shugabannin kananan hukumomin ne ba tare da bin dokar kasa ba inda ya rushe zababbun dukkansu baki daya a ranar 10 ha watan Yuli 2015 ya kuma maye gurbinsu da kwamitin riko a kowace karamar hukuma da ke Jihar.
Kungiyar ta kuma yi bayanin cewa gibin da aka samu sakamakon daukar wannan matakin aka rika tafiyar da harkokin kananan hukumomin ta hanyar da ta sabawa doka, kuma har yau wadansu shugabannin bangare ne ke shugabantar kananan hukumomin a Jihar baki daya.
A cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata ranar 20 ha watan Janairu 2020 da shugaban honarabul Ibrahim Lawal Dankaba ya sanyawa hannun suna koke ga ministan shari’a a kan ya Sanya baki game da lamarin, honarabul Dankaba ya koka a kan irin tabarbarewar tattalin arziki, harkokin tsaro da na jin dadi da walwalar jama’a a cikin Jihar abin da ya ta’allaka da rashin samun zababbun shugabannin kananan hukumomi kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin mulki sashi na 7(1) colin baka na kundin tsarin Mulkin shekarar 1999 amma kuma an sabawa wannan sashin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.