Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar tuntuba ta matasan arewacin Najeriya (AYCF), da ke kan gaba wajen kare muradun al’umma marasa galihu da kasa baki daya, ta bayyana da kakkausan lafazi inda ta yi Allah wadai da kokarin mayar da babban birnin tarayyar Najeriya koma baya, ta hanyar mayar da wadansu muhimman bangarorin babban Bankin Najeriya da kuma hukumar kula da tashi da sauran Jiragen sama ta kasa zuwa birnin Legas tsohuwar hedikwatar Najeriy.
Kungiyar tuntuba ta matasan ta ce hakika wannan kokarin a mayar da wadansu muhimman bangarorin Gwamnati zuwa Legas zai zama barazana ga matsayin Abuja na hedikwatar kasa kuma hakan zai yi wa kasar barazana.
Shugaban kungiyar tuntuba ta matasa zalla (AYCF) na kasa Shettima Yerima, ya bayyana damuwarsu ne saboda irin illar da lamarin zai jewo sakamakon mayar da wasu bangarorin gwamnati Legas.
Sai ya kara jaddada cewa hakika wannan kokarin tayar da wasu bangarorin Ma’aikatun Gwamnatin tarayya zai iya kawo matsala ga hadin kan kasa, ya kuma lalata ayyukan na Gwamnati,ya kuma mayar da harkokin tattalin arziki baya da kuma samar da matsaloli ga batun yankunan kasa da ake da su a halin yanzu.
Kamar yadda Shettima ya bayyana cewa tin da dadewa magabata sun zabi Abuja ne domin ta zamo sahihiyar hangar hadin kan kasa a kuma samu ainihin dai- daiton da ya dace a samu game da matsugunnin ma’aikatu da hukumomin Gwamnati.
Saboda haka dukkan abin da za a yi domin a samar da nakasu ga wannan tsarin da ake da shi hakika kungiyar AYCF ba za ta lamunta ba kuma za ta ci gaba da kalubalantar shi ita da mambobinta Bali daya.
Shettima ya kuma Soki irin yadda wadansu mutanen arewacin Najeriya suka yi shuru game da wannan batun kwashe Ma’aikatun Gwamnati a mayar zuwa Legas, musamman ma ga yan Boko wanda harkar Gwamnati ke amfanatsu a koda yaushe kuma suka san dadin ta.
A dai dai lokacin da batun tattalin arziki da harkokin siyasar arewacin Najeriya ke cikin wani mawuyacin yanayi ba dace ba yan Bokon yankin suyi shuru saboda dole ne yan kasa su tashi tsaye wajen yin magana a game da haifarwa yankin Arewa matsala.
Sai Shettima Yerima ya yi kira ga daukacin hukumomin da wannan lamarin ya shafa da su canza tunanin da suke yi, musamman ganin irin yadda lamarin zai haifarwa da Abuja matsala a matsayinsa na babban birnin tarayyar kasa.
Kungiyar ta bayar da shawara ga mahukunta da su mayar da hankali a game da ayyukan da za su hada kan kasa, kuma a dauki mataki a kan wadanda ke kokarin aiwatar da wannan aikin da zai zamarwa kasa matsala ta fuskar siyasa da tattalin arzikin yankin arewacin kasa.
Kungiyar AYCF ta kara da jaddada kudirinta na ci gaba da samar da zaman lafiya da ci gaban arzikin al’ummar kasa baki daya, ta kuma lashi takobin cewa za ta ci gaba da kare batun birnin tarayya tantama shi ne babban birnin tarayya da ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin tarayya za su ci gaba da kasancewa a wurin, kuma kungiyar da mambobinta ba za su ta ba lamuntar kawo wa birnin tarayya duk wata matsala ba.