Home / Big News / Kungiyar Hadin Kan Hausa Da Hausawan Duniya Ta Yi Babban Taro A Kaduna

Kungiyar Hadin Kan Hausa Da Hausawan Duniya Ta Yi Babban Taro A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
Suleiman Yahaya Babangida wanda shi ne cika Soron Mina, kuma wani babban jigo a kungiyar hadin kan Hausawa da Hausa a duniya ya ce idan an lura a tarihin Najeriya da arewacin kasar kowa ya san muhimmancin Kaduna a matsayin babbar cibiyar arewa.
“Mai Martaba Sarkin Musulmi ya ta ba shaida mana cewa taron Gwamnonin arewacin Najeriya shima a Kaduna ake yi shi yasa wannan kungiyar ta zabi bari ta yi taro a Kaduna ta gabatar da shugabannin ta saboda Kaduna wata babbar cibiya ce ta arewacin Najeriya idan an lura mai girma Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato a Kaduna ya zauna har Allah ya dauki ransa duk da yake a wannan lokacin ba a haife mu ba, amma muna bin tarihin iyayen mu manya wanda kamar Mai alfarma Sarkin Musulmi Marigayi Dasuki ya kan ba mu cikakken tarihin yadda abin yake har na Sardauna. Shi yasa a matsayi na na mataimakin shugaban kungiya da na fito daga gidan Sarauta guda Uku da gidan Wazirin Katsina Haruna da kuma gidan Sarkin Zamfara Aliyu Sambo Sarkin Zurfi da kuma a akwai Kakaninmu da aka aura a wannan gida diyar Sarkin Musulmi Hassan Dan Ma’azu wadda ta haifi mata a wurin Sarkin Zamfaran Zurfi Sule to, dole ne mu mutunta wadannan gidaje mu mutunta Sarauta don haka ne muka yi wannan taron a Jihar Kaduna”.
Cikasoron Minna ya kuma shaidawa manema labarai dalilin manufar kafa wannan ƙungiya inda ya ce manufar ita ce a taimakawa Almajirai, Marayu da Nakasassu da kuma matan da mazajensu suka rasu suka barsu sannan kuma ya’yan kungiyar su taimakawa Gwamnati da fadakar da yara Matasa da iyaye su dawo da tarbiyya da al’adun Malam Bahaushe ba wata manufar da ta wuce hakan.
A game da wasu bakin al’adun da suka shiga cikin malam Bahaushe kuwa sai Cikasoron Minna ya ce hakika za su yi iyakar kokarinsu wajen fadakarwa domin su har yau a gidajensu ba su amince da irin wadannan abubuwan ba don in Ka lura na zo wannan wurin da riga da alkyabba da Rawani kuma duk wadanda na gayyato a wannan wurin na gayyato iyalan Dan kwairo ne wanda har shi mawakin na sanya masa babbar riga na kawo Rawani na kawo alkyabba na sanya masa hakan ke nuna cewa wannan ƙungiya fa na son ta dawo da manufar da aka yi asarar ta wadda babbar asarar ce da malam Bahaushe ya bar al’adarsa da ya gada iyaye da iyaye ta tabarbare.
Ya kara da cewa yau shekaru biyar kenan da kafa kungiyar, Hadin kan Hausawa da Hausa da ya ce sun samu gagarumin ci gaba domin ko a wajen wannan taron an taimaka da kudi da abinci da za a ba mata guda sittin kuma a gobe kuma za a taimakawa Almajirai da za a ba su kayan Gyaran Takalma ( shoe maker), za kuma a ba wasu kayan yanka kumba zakuma mu ba wasu mata kayan jarin abinci na Shinkafa da Wake su fara sana’a haka ma a Zariya.
Ya ci gaba da bayanin cewa ita wannan ƙungiya ta na a kasashe a ƙalla sama da Hamsin na duniya, kuma ta hanyar kungiyar nan ana Ceton mutanen da suka shiga cikin wani hali.Ko a Minna akwai Dan kungiyar nan da yaje kasar Benin Republic a Kwatano da ya samu matsala muka duba ba laifi ya aikata ba an bashi Daurin Rai da Rai amma ya yi shekaru Uku muka ceto shi kuma shugaban kungiyar na kasar Benin Republic ya biya masa tarar Naira miliyan daya kunga wannan mutum ba mu san shi ba ba mu taba ganinsa ba amma saboda ya na bahaushe ne ya taimaka mana kuma akwai lokacin da muka yi bakin Hausawa da suka je Ghana shi shugaban wannan kungiyar haka muka sanya ya ba su masauki don haka akwai abubuwa da dama da suke faruwa na taimako dalilin wannan ƙungiya. Ko mu daga Minna da Najeriya abubuwa na faruwa da muke taimakawa da yawa muna ceto su muna yi akwai ma inda zaka ga yara kananan suna yin almajiranci sai mu nemi iyayen yaran mu tsawata har ma akwai lokacin da aka sayawa wani mutum uban wasu yara aka saya masa KeKe Napep aka bashi duk ta wannan ƙungiya sannan kuma muna yin addu’o’i ga kasa baki daya.
” Ko a yau da zamu fara wannan taron sai da aka sauke Alkur’ani mai tsarki domin kasar nan Najeriya ta zauna lafiya da kuma dukkan kasashen Musulmi su zauna lafiya shi yasa aka ce Kungiyar Hadin Kan Hausa da Hausawan duniya  babu kabilanci a ciki India kana jin Hausa zamu ta fi tare da kai kuma ko mutum ba addinin musulunci yake ba za mu taimaka masa domin ba inda addinin ya hana ko ya haramta a taimakawa wanda ba Musulmi ba don haka ba mu kyamar Kuturu, Makaho kuma ba mu kyamar Talaka kuma ba mu shiga harkar Siyasa.

About andiya

Check Also

Why Yakubu Dogara Is Claiming Nigeria Is On The Right Track

By Imrana Abdullahi Nigeria is drowning while Rt. Hon. Yakubu Dogara smiles from the comfort …

Leave a Reply

Your email address will not be published.