Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Kwadago, Yan Najeriya Sun Yaba Wa Ahmad Musa Dan Giwa 

Kungiyar Kwadago, Yan Najeriya Sun Yaba Wa Ahmad Musa Dan Giwa 

Mustapha Imrana Abdullahi
Yayan kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna tare da daukacin yan Najeriya sun bayyana cikakkiyar gamsuwarsu da irin yadda shugaban Bankin bayar da lamunin gina wa, gyaran gidaje na kasa mazayyani Ahmad Musa Dan Giwa saboda ci gaban da ya kawo ma kasa.
Shugabannin kungiyar kwadagon da wasu yan Najeriya da suka je domin yin hudda da Bankin bayar da lamunin gina gidaje ko gyaransu a babban  ofishinsa da ke Abuja fadar Gwamnatin tarayya, kamar yadda suka fayyace wa duniya cewa sun je ofishin nasa da niyyar mai yuwuwa su yi a kalla kwanaki hudu ko biyar kafin su ga shugaban Bankin Ahmad Musa Dan Giwa, amma abin mamaki da zuwansu aka gaya masa nan take aka ce masu su shiga.
Sun bayyana hakan ne a wajen taron ranar Bankin da aka yi a kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna, inda suka ce wannan lamari ya ba su mamaki domin ba su ba kowa ko sisin Kwabo ba nan da nan kuma suka gan shi ido da ido kuma bukata ta biya.
“Mu ma’aikata hakika jagorancin Ahmad Musa Dan Giwa ya amfane mu domin mun samu damar mallakar gidaje kuma mun samu makudan kudin da Bankin ke bayarwa domin yin gyaran gida ba tare da shan wata wahala ba ko bayar da kudi ga wani mutum ba”, inji yan kwadago.
Suka ci gaba da cewa “mun san babu maganar batun cin hanci ko rashawa idan mutum ya je neman kudin ginin gidaje ko gyaran gida da sauran abin da Bankin ke yi, don haka ban da jagorancin Bankin kuma ya na jagorancin hana cin hanci da karbar rashawa”.
Sakamakon irin wadannan halaye na karamci da iya aikin Mazayyani Ahmad Musa Dan Giwa muke yi masa godiya kuma muna mika sakon godiya ga shugaba Muhammadu Buhari da ya na da wannan mutum ya shugabanci wannan Bankin.
Kuma jama’ar da muka tattauna da su sun yi kira ga Ahmad Musa Dan Giwa da ya hanzarta yin bayani a kan mataki na gaba musamman irin kokarin da mutane ke yi a Jihar Katsina na sai ya tsaya takara domin ya ci gaba da rikon da yake yi masu a halin yanzu.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.