Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Marubuta A Kafofin Yada Labarai Sun Karrama Fasto Yohanna Buru

Kungiyar Marubuta A Kafofin Yada Labarai Sun Karrama Fasto Yohanna Buru

Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar marubuta a kafofin yada labarai mai su na Arewa Media Writers sun Karrama sanannen Fasto Yohanna Buru, sakamakon irin ayyukan tabbatar da zaman lafiya da Malamin addinin Kiristan yake aiwatarwa domin samun ingantar zaman tare da Juna.
Yayan kungiyar sun bayyana cewa sun yi shawarar bashi wannan lambar karramawa ne duba da irin yadda Malamin addinin Kiristan ke aiwatar da ayyukan jin kan jama’a cikin unguwanni,kasuwanni da sauran wuraren da mutane ke rayuwa ba tare da nuna wani bambanci ba, fatansa dai kawai a samu zaman lafiya da taimakon Juna.
Yayan kungiyar sun ce babban dalilin da yasa suka kafa wannan kungiya shi ne domin fadakarwa ga mambobinsu su san abubuwan da yakamata a rika rubutawa a dandalin Sada zumunta musamman ganin irin yadda ake samun matsalolin yada labarai marasa tushe balantana makama wanda hakan ya saba da tanaje tanajen aikin yada bayanai ga jama’a.

About andiya

Check Also

Trafficking: NAPTIP seeks more collaboration, advise potential victims

  By Suleiman Adamu, Sokoto The National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person(NAPTIP) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.