Home / KUNGIYOYI / Kungiyar NASWDEN Ta Karrama Kwamared Aminu Hassan

Kungiyar NASWDEN Ta Karrama Kwamared Aminu Hassan

Daga Imrana Abdullahi

Kwamared Aminu Hassan jigo ne a gamammiyar  kungiyar  yan jari Bola ta kasa (NASWDEN) ya bayyana gamsuwa da irin yadda gamammiyar kungiyar ta ga kokarinsa har suka bashi lambar karramawa.

Ya ce hakika shugabanci yi wa jama’a aiki shi ne shugabanci a kowane irin mataki ne da mutum ya tsinci kansa a ciki, “a gaskiya ni ban san ma za a Karrama ni ba, amma mutanen Jihar Kaduna yayan kungiya suka ga irin jagorancin da ake yi masu shi yasa suka Karrama ni domin cancantar da suka gani na a ba ni lambar karramawa don haka Ni ma ba za ta lamarin ya zo Mani kawai aka kira suna na saboda haka ina godiya da wannan karramawar da Jihar Kaduna suka yi mani”.

Kamar yadda na fadi a cikin jawaban da na yi ita fa sana’ar Gwangwan da ake ga ni kusan ta na daya daga cikin sana’ar da take juya tattalin arzikin kasar nan wadda na ce duk masana’antun Najeriya kashi Saba’in daga cikin dari na Ma’aikatun kayan Bola ne ake sarrafa wa ayi sababbi da su to, bijirowar wadannan kamfanoni na matsa karfe da kuma na Narka karfan, wato akwai bambanci saboda shi na matse karfen yan Canis ne suke zuwa su matse karfen su ta fi da shi. Shi kuma na wannan kamfanin karfe na Katsina da ya koma a hannun yan “NAK”, kamfani ne da ke narkawa da kuma yin karfen ayi sabon rodi, amma saboda yanayi na sayar da kamfanonin Gwamnati aka sayar wa su mutanen mu. Bayan da a can baya an sayar wa da kamfanin Dana guruf da suka kasance indiyawa ne, amma a halin yanzu sai Allah ya dawo da shi hannun mutanen mu na Arewa wato “NAK Guruf”, wato su Alhaji Akilu Hassan Sardaunan Funtuwa, da a yanzu suka mallake shi saboda haka alfanun kamfanin na farko shi ne muma mun samu kamfanin sarrafa karfe a arewacin Najeriya da wannan ne nake tabbatar da cewa a duk  yankin Arewacin Najeriya ma daga Ilori sai Abuja ne kawai ake da kamfanin sarrafa karfe don haka ba karamin ci gaba ba ne aka samu kasancewar duk sun rufe.

” hakika akwai saukin da aka samu saboda ace wai sai an dauki kaya an kai Kudu a can baya sai ga shi a yanzu an samu a nan gida arewacin Najeriya, a nan za a yi kayan wato a narka karfan sannan kuma a kawo mana kayan mu saya kum mu sayarwa da kasashe makwabta irin su kasar Kamaru, Nijar da Cadi”.

Sai Kwamared Aminu ya ba su shawara kamar haka cewa lallai ya dace kowa ya Sani fa ita wannan sana’ar ta na da hadarurruka da tsautsayi da ke fada wa mambobinmu domin wani lokacin za a kawo maka kaya baka Sani ba kayan na laifi ne, ina kira ga mutanen mu su Sani cewa lallai su kiyaye a kan abin da za su saya duk abin da za su saya suka ga na laifi ne su kiyaye shi. Babu hannun mu a cikin aikata laifi ba mu goyon bayan aikata laifi kuma muna kira ga yan kungiya da su kiyayi sayan kayan da ya kasance na laifi. Kuma muna da tabbacin cewa zai yi wahala kaga dan kungiyar nan ya na sayan kayan laifi wasu baragurbi ne kawai suke ketowa cikin mu, suma muna ta kokari iya kokari mu fitar da su daga cikin mu baki daya

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.