Home / Labarai / Kungiyar Yan Fansho Sun Yaba Wa Gwamnan Kaduna

Kungiyar Yan Fansho Sun Yaba Wa Gwamnan Kaduna

  1. Kungiyar Yan Fansho Sun Yaba Wa Gwamnan Kaduna
  2. Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda Alhaji Alhassan Balarabe Musa ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kammala shirin biyan wadanda suka ajiye aiki sama da mutane dari biyar (593) kudin Graduti
¬†Mutanen da abin ya shafa sune wadanda suka yi ritayar a shekara 2015 daga cikin ma’aikatan Kananan hukumomi, a bangarori irin na Ilimi, Ma’aikatar shari’a, hukumar samar da ruwa ta Jihar Kaduna, hukumar kulawa da gine gine ta KASUPDA, Ma’aikatan ayyuka, ma’aikatan tara kudin shiga, ma’aikatar kula da kananan hukumomi, kwalejin ilimin Kimiyya da fasaha da kwalejin ilimi ta gidan waya da dai sauransu.
Bisa wannan kokari ne yasa kungiyar masu karbar fanshon suke godiya ga hazirkin Gwamnan bisa wannan kokarin da yake yi a halin yanzu.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.