Home / Labarai / Gwamnan Bauchi Bala Muhammad Ya Rabawa Musakai Kekunan Hawa

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad Ya Rabawa Musakai Kekunan Hawa

Imrana Abdullahi

 

A kokarin ganin annsamawa musakai da ke fama da nakasa domin su samu saukin rayuwa yasa Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi rabawa masu fama da nakasa Kekunan hawa irin na guragu saboda su samu saukin gudanar da harkokin rayuwa.

Kamar dai yadda Gwamnan ya yi wa jama’a alkawari cewa zai yi iyaka bakin kokarinsa domin taimakawa jama’ar Jihar Bauchi su samu saukin rayuwa wannan wata manuniya da kowa zai shaida Gwamna Bala Muhammad na iyakar kokari ya cika alkawarin da ya yi wa mutanen Jihar Bauchi.

Kamar yadda muka samu tattaunawa da wadansu mutane a ciki da wajen Jihar Bauchi sun shaida mana cewa ba su ma taba ganin irin wadannan Kekuna da Gwamnan ya rabawa musakan ba domin kuwa a cewarsu Kekuna ne irin na musamman da ke tafiya da zamani.

 

Da suke bayyana zuciyarsu wadanda suka amfana da taimakon Kekunan sun yi ta bayyana farincikinsu da abin da Gwamna Bala Muhamad Kauran Bauchi ya yi masu, a kokarinsa na sama masu saukin rayuwa.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.