Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Yan Kasuwa Na Fadakar Da Jama’a Game Da Cutar Korona

Kungiyar Yan Kasuwa Na Fadakar Da Jama’a Game Da Cutar Korona

Imrana Abdullahi
Hadaddiyar kungiyar yan kasuwa shiyyar Funtuwa karkashin Alhaji Musa Shugaba sun dukufa wajen wayar da kan jama’a game da cutar Covid – 19 da ke yi wa duniya barazana.
Hadaddiyar kungiyar yan kasuwar na shiyyar Funtuwa sun shiga bakin kasuwar da ke makera Funtuwa suna fadakar da mutane kan matakan da ya dace su dauka domin kaucewa yaduwar cutar a tsakanin al’umma musamman masu cin kasuwa.
Da yake tattaunawa da wakilinmu Alhaji Musa Shugaba ya bayyana mana cewa sun shirya wannan taron gangami ne domin fadakar da jama’a kan yadda za su gujewa cudanya tsakanin jama’a, yadda jama’a za su yi amfani da abin wanke hannu ko sabulu da kuma yin amfani da Takunkumi domin kare lafiyarsu baki daya.
“Mun zabi wannan kasuwane ta bakin asibitin Funtuwa domin fadakar da jama’a kan illar da ke tattare da cakuduwar mutane a cikin halin da ake ciki na matsalar cutar Korona a kan yadda lamarin yake a duniya baki daya”.
Ya ci gaba da cewa yin wannan fadakarwa wajibi ne domin irin yadda lamarin Korona yake ba shakka sai da wannan fadakarwa saboda jama’a kowa ya farga a kan abin da ya dace ya yi

About andiya

Check Also

TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

Daga Imrana Abdullahi Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.