Home / News / Kuskure Ne Cewa Mulki Ya Koma Kudu – Kwankwaso

Kuskure Ne Cewa Mulki Ya Koma Kudu – Kwankwaso

Imrana Abdullahi
Shugaban darikar siyasar Kwankwasiyya na duniya Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kururuwar da wadansu suka yi har da jam’iyyar APGA na mulki ya koma Kudu cewa babban kuskure ne can a gare su da suke yin wannan ikirarin mulkin ya koma Kusu.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da tashar Talbijin ta Farin Wata a cikin shirin “Ina Muka Dosa”.
Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa akwai misalan siyasa da yawa da suka faru a tarihin siyasar Najeriya misali kamar lokacin da Abiola ya tsaya takara shi a matsayin sa na dan Kano a Unguwar da yake a wancan lokaci na Gandun Albasa akwai shugabansu Bashir Tofa ya na zaune ne a unguwar Gandun Albasa amma sai da ya tsaya SDP na lashe zaben a akwatinsa da karamar hukuma da kuma Jihar Kano baki daya SDP ta lashe zaben suka bar shugabansu Bashir Tofa da ke takarar shugaban kasa a wata jam’iyya.
Kwankwaso ya ci gaba da cewa akwai misalin lokacin da Obasanjo na takara duk da yan uwansa ba su son shi amma aka ta fi Jos aka fafata sula tabbatar Obasanjo ya kai labari ya lashe zaben ya zama dan takarar shugaban kasa kuma ya ci zaben shugaban kasar duk da yan uwansa ba sa son shi, don haka ya dace su tabbatar sun yi abin da ya dace.
“Hakika kuskure ne can a wajensu da suka yi wannan ikirarin na cewa mulki ya koma Kudu amma muna fatar za su gyara kuskuren”, inji Kwankwaso.
Ta yaya wadanda ba su san yadda za su share Daji ba su tabbatar sun gina gida mai kyau sai ku rika yin abin da suka ga dama da sunan mulki.
Sanata Kwankwso ya ci gaba da cewa siyasa fes take lafiya kalau take, sai dai kawai shugaba dole ne ya zama mai zura idanu a koda yaushe domin idan wani abu ya shigo da ba a san sa a kaishi kasa ta yadda za a samu ci gaban da kowa ke bukatar samu.
A game da batun matsalar tsaro shi ne sai an zura idanu sosai domin yin maganin masu laifi.
Mafi yawa an san masu Yakin nan na sari ka noke, ko a lokacin ina Gwamnan Jihar Kano sai da muka yi masu ratata domin ba mu amince kowane batagari ya shigo Jihar Kano ba

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.