Home / News / Shugaban PDP Ya Kalubalanci El-Rufa’I

Shugaban PDP Ya Kalubalanci El-Rufa’I

Shugaban PDP Ya Kalubalanci El-Rufa’I

Mustapha Imrana Abdullahi

Shugaban jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna Felix Hassan Hyet, ya kalubalanci Gwamnan kaduna Nasiru Ahmed El-Rufa’i bisa irin yadda yake gudanar da al’amuran tafiyar da mulki a Jihar ba tare da kula ko yin amfani da tanajin doka da girmama jama’a ba wajen gudanar da dimbin Abubuwa a Jihar.

Ya ce mutane na bukatar wanda ke ganin girma da darajar mutane wajen tafiyar da dukkan tsare tsaren Jihar wanda hakan zai bayar da damar cewa an damu da abin da suke ciki.

Hyet, ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da yan kwamitin da aka Dorawa nauyin zuwa a sasanta yayan jam’iyyar da kuma dai-daita al’amuran jam’iyyar domin fuskantar kalubalen zaben da ke tafe nan gaba, a shekarar 2023.

Ya kuma bayyana irin yadda PDP ta kammala shirin karbar mulki a matakin Jiha da kuma kasa baki daya, iron yadda APC ta gaza wani lamari ne a fili da ke nuna cewa jam’iyyar PDP tare da yayanta za su samu damar lashe zabe cikin sauki a dukkan matakai, a shekarar 2023 mai zuwa.

Tsohon ministan zirga zirgar Jirahen sama ya tabbatar wa da yayan PDP cewa da yawan mutanen Jihar kaduna sun kosa lokacin zabe ya zo domin kawar da APC sakamakon irin yadda ake keta hakkin jama’a wajen gudanar da lamurra kuma ba a duba na can kasa a dukkan abin da ake yi.

Shugaban na PDP ya kuma bayyana rashin tabbas ga hukumar zaben Jihar Kaduna a kan ko za ta yi wa sauran jam’iyyun adawa adalci a lokacin zaben kananan hukumomi.

Inda ya ce an yi wa Jam’iyyarsa makudi a zaben kananan hukumomin da ya gabata karkashin Gwamna El- Rufa’I. Sai ya yi kira ga Gwamnan da ya tabbatar da ya yi aiki da rantsuwar da ya dauka domin tabbatar da yin aiki da kundin tsarin mulkin kasa.

He charged chairmen and committee members to carry out their assignments With diligence, commitments and loyalty for progress and unity of the party ahead 2023.

Shehu Bawa ABG shi ne wanda aka nada ya jagoranci dai-daita al’amuran jam’iyyar ya kuma bayar da tabbacin cewa zai yi aiki domin samun nasarar da ake bukata musamman ganin irin yadda aka dora masa wannan aikin.

Ya kara da cewa PDP ce kawai jam’iyyar da za ta saita lamuran kasar nan tun daga Jiha zuwa Gwamnatin tarayya.

Tsohon dan majalisar ya shawarci yan Nijeriya da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga shugabancin, lamuran tsaro kuma jama’a su duba sosai domin tantance irin yadda lamarin tattalin arziki yake da kuma halin tsaro a zamanin Gwamnatin PDP, ya kuma ce yanayin da ake ciki a zamanin PDP mutane na iya cin abinci sau uku a rana sabanin irin yadda lamarin yake a halin inda jama’a ba su iya samun damar cin abinci sau uku wasu ma ko sau dayan ma sai a hankali.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.