A Kaduna, Imrana Abdullahi
Gabanin fara aikin kasuwar bakindogo da ke cikin garin kaduna tawagar kwamitin da aka kafa domin aikin rage cinkoso ya ziyarci kasuwar bakin dogo.
Shi dai wannan kwamitin na karkashin jagorancin kwamishinar ma’aikatar gidaje da bunkasa birane masaniyar harkar taswirar Zane Zane Fausat Ibikunle, sun tabbatar da kai wannan ziyara ne gabanin fara aikin.