Home / News / Kwankwaso Na Kan Kujerar Gwamna Na Kada Shi -Shekarau

Kwankwaso Na Kan Kujerar Gwamna Na Kada Shi -Shekarau

 Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa in ba a manya ba tsohon Gwamnan Kano Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso na kan kujerar Gwamnan Kano amma ya kada shi don haka shi bashi da wata jayayya a tsakaninsu.
Ya bayyan haman ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a inda ya ce hakika tsakaninsu da Kwankwaso babu wata ja inja.
“Mudai abin da muke kokarin gani a koda yaushe shi ne tabbatar da yin harkokin da za su kara inganta harkokin rayuwar jama’ar da suke tare da su kuma suna kokarin kaucewa duk wani abu da zai iya kawo wa mutanensu cikas a dukkan al’amura
Ya ci gaba da cewa ko a lokacin da suka kafa jam’iyyar APC ba wai suna jayayya da Kwankwaso bane sai dai kawai sun yi ta kokarin a sauna domin daidatawa tsakaninsu da suka kirkiro jam’iyyar APC da kuma bangaren Kwankwaso a lokacin da suka shigo APC lokacin su Kwankwason suna da Gwamnati don yi wa kowa adalci.
A tsakaninsa da Muhammadu Buhari kuwa shima ya tabbatar wa manema labarai cewa ya yi hakika babu wani abin da ya wuce girma da arziki a tsakaninsu, a game da batun ko yana ba Buharin shawara kuwa shekaru ya ce lamarin bada shawara wani lamari ne da yake tattare da yanayi in an samu dama wannan ba matsala brace
Ya kara da bayanin cewa ko a shekarar 2011 shi ya yi wa jam’iyyar ANPP takarar shugaban kasa yayin da shi kuma Buhari ya tsaya takarar karkashin CPC kuma har yanzu dangantaka na nan daram.
“Saboda tun a farko muna ANPP tare sai Buhari yaga dacewar ya fita domin kafa CPC kuma ya yi mata takarar shugaban kasa kuma an kafa APC tare da ni”, inji shekarau.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.