Home / Idon Mikiya / LABARIN DAN KASA A TURAI – KASHI NA DAYA

LABARIN DAN KASA A TURAI – KASHI NA DAYA

GABATARWA: Ya masoya kuma ma’abota karatun adabin Hausa, godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya nuna mana wannan rana da zamu fara rubuta sabon littafi tare da ku. Wannan labarin naku ne, saboda kune kuka bada shawarar cewa a rubuta shi. Saboda haka masu waya a yi tanadin DATA da caji saboda akwai nishadi sosai a gabanmu. Ina kuma godewa Usman Kabara wanda shima ya taka rawa wajen gani wannan labarin yayi rai kuma ya kayatar, mahaifiyata UMMA (HALISA) GALADANCHI saboda rayuwa da tarbiyya da ta bamu, da kuma soyayyar adabin Hausa. Jama’a tambayar anan itace kun shirya? Saboda na riga na daura dammara, motar nan tare daku zata hau titin adabin Hausa. Zamu yi dariya, zamu karu, zamu ji haushi, zamu kara ilimi, sannan kuma zamu gir-giza kai. Allah Ya ji kan marigayi Alhaji Ali Makaho yace “Rayuwar dan arewa a Turai”, Chali Boyi yace “abun ba dadi dan Garba”.

INDA ZA’A FARA: “Ranar da na fara zuwa Amurka, ko turanci bana ji. In banda jifa-jifa dan abunda na koya a Firamari. Amma tunda naje kasar yarabawa da inyamurai na sayar da robobi da goro da kilishi ba tare da gane abunda suke fada ba, ai kuwa duk inda naje a duniyannan sai dai wani Ikon Allah. Amma sai na samu abunda nake nema da ikon Rabbis Samawati. Hular dake kaina irinta ake cewa TASHI KA FIYA NACI, Aminu Mai Shayi Taraba ne ya sayo mun ita a lokacin da yaje aikin Hajji shekaru 8 da suka gabata, amma har yanzu akwai wadanda suke tunanin sabuwa ce. Ina ji da ita. Masu magana suka ce “abu naka maganin a kwabe ka”. Ga jellabiya na sha kamar tukari daga Jidda. Hankali na kwance, saboda na shirya komai, kuma na san ba zan wahala ba, zan samu biyan bukata in Allah Ya yarda, sannan in koma gida.”

“Kun gani ko, idan na samu waje surutu ne da ni kamar famfon da ya lalace, ko sunana ba gaya muku ba, na tsunduma cikin labari sai kace wani BBC. Sunana Kameel Usman Chazali, amma an fi kirana da Dan Kasa. Na san zaku so kuji dalilin da yasa ake ce mun haka, amma sai anjima zamu taba wannan. Babu shakka, ni dan Kano ne a arewa, sai dai babu lokon da ban shiga ba a Najeriya. Na yi sana’o’i sun fi talatin, amma duk abun nan da nake gaya muku, a Amurka aka haife ni. Mahaifina ya taba zuwa karatu karkashin tallafin marigayi Audu Bako da iyalinsa, aka haife ni amma ina dan jariri muka koma. Tun lokacin ban dawo ba. Kun san halin Najeriya, da kyar baban nawa ya samu aiki, sannan daga baya ya watsar ya kama sana’ar wanki da guga a gidan gwamnati. Can da ya ga abun babu wani cigaba, sai yayi watsi da shi ya bude tireda. Da tiredar ta bunkasa sai ya koma kantin kwari yana sayar da takalman yara da dan kunne. Na san yanzu kun fara fahimtar dalilin da yasa nima nayi sana’o’i sun fi 30. Masu magana suka ce “kyan da ya gaji ubansa”. Amma zuwan mutanen Chana ya karya shi, shine ya koma karantar a makarantar allo, sannan idan limamin unguwar mu ya tafi hajji, ko baya jin dadi, sai baban nawa ya ringa jan Sallah. Kar na cika ku da surutu, bari mu cigaba. Har yanzu ni ban gane amfanin karatun boko ba, na san mutane da yawa suna kammalawa suna samun aiki a gwamanti, ko kamfanoni, amma ni ba’a nan zuciyata take ba. Ina son hulda da jama’a, sannan ina sha’awar kiwo. Mahaifiyata tayi shekaru 14 tana kiwon kaji, kuma har sai da ta kai ta kawo na san komai game da kiwon kaji. Daga irin abincin da yafi musu kyau, zuwa magunguna, da kiwo, da kwai, zuwa aure, da yankawa, da soyawa, ko dafawa, ko kuma farfesu irin wanda aka fi sani da “pepper chicken”.

“Kwanci tashi, aka kawo wani abu wai shi ‘demokradiyya’ bayan saukar Janar Abdusalamu Abubakar, mu dai a gidanmu kallo ne namu, saboda a lokacin bamu damu da gwamnati ba. Idan aka ce demokradiyya har kyalkyace wa muke yi dariya, jinshi muke kamar wani kwalin ashana. Kwanci tashi, mutanen Najeriya sukayi batan kai, suka zabi wani mutum wai shi Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa. Wannan lokaci ne kowa ya fahimci amfanin gwamnati da yadda al-amuranta suke da nasaba da rayuwar yau da kullum. In takaita muku, kunci da talauci ya yawaita, ga zub da jini, muka fara diban kaji muna sayarwa domin siyan masara. Bugu da kari wata cuta da ake cewa “murar tsuntsaye” ta kawo ziyara gidanmu ta karashe ragowar kajin. A unguwar Gwammaja muke, kusa da Kofar Ruwa a layin ‘Yan Faranti. Muna ji muna gani, wasu mutane sanye da wasu ledoji ruwan dorawa suka shigo gidanmu, suka kwashe ragowar kajin mu suka zuba a cikin buhu suka yi gaba da su. A nan ne ido ya raina fata. Dama ni kafinta ne a lokacin, ina siyo katako a kasuwar Kofar Ruwa ina hada kananan kujeru da mata ke amfani da su, ina sayarwa. Ranar da murar tsunsaye ta yi wa gidanmu maraba, to wannan rana ce idanu na suka raina fata. Na san cewa aikin kafinta ba zai biya bukatun mu ba. Gashi nine babban nimiji a gidan. Dole na sake lissafi.”

Sai mika wuya yake, ya kalli nan, ya kalli can. Tun da yake bai taba ginin gine-gine da gadoji kamar haka ba. Ga shi babu leda ko roba ko shara a gefen titi. Kamar an wanke titunan da ruwa da sabulu. Baturiyar dake tuka motar sai hira da dariya take yi da baturen dake daya bangaren direba a zaune. Shi kuwa Dan Kasa yana baya, ya waiga nan, ya waiga can. Gashi baya jin abunda suke fada balle ya fahimci turancin da suke. Sai baturen ya jiyo yace da Dan Kasa “Paper”. Dan Kasa ya gane me yake nufi, sai yayi sauri ya saka hannu a aljihu ya dauko takarda ya mikawa bature. Bature ya mikawa baturiya dake tuka mota ta karanta. Sai ta juyo ta kalle shi. Dan Kasa kuwa bai san me suke nufi ba. Shi dai abunda ke gabansa yanzu shine kashe kwarkwatar idanunsa. Abunda yake bashi mamaki shine duka motocin garin fes suke, da wuya ka ga mota mai kwarzano daya a jikinta, balle a ce tana hayaki ko kara. Gashi kowace mota gudu take kamar zata bar garin. “Abun kamar fim” ya fada a zuciyar shi. Da bature da baturiya sun yi hira, sun yi dariya, sai bature ya juyo wajen Dan Kasa ya daga hannunsa na dama yace “HIGH 5”, wato a tafa kennan. Shi kuwa Dan Kasa shima ya daga hannu, ya wangame baki yace “HIGH 5” su kashe. Duk dadi ya ishe shi. Turawa na sonshi. Masu magana suka ce “Juma’a mai kyau, tun daga Laraba ake gane ta”.

Da suka shigo birnin Washington D.C, sai baturiya ta ja mota a kusa da wani dogon gini ta tsaya. Suka juyo suka kalle shi, suka ce “HERE”. Shi Dan Kasa yana gani anyi haka, ya san cewa ajje shi zasu yi. A lokacin ya yunkura, ya bude kofar mota ya fita waje rike da Ghana-Must-Go dinshi.

Wato baturen nan a gefen Dan Kasa ya zauna a cikin jirgi da suke tahowa daga Cairo. To tun wannan lokacin ne suka shaku duk da cewa babu wanda yake gani abunda dayan ke fada. Amma jininsu ya hadu. Bayan mikawa baturen takardarsa ya karanta, sai bature ya ja hannunshi bayan sun fito daga tashar jirgin sama ya nuna mishi cewa zai rage mishi hanya. Ba su jima a waje ba, baturiya ta iso shine suka shiga mota, suka yi gaba.

Yanzu kuma gashi turawan zasu tafi, bayan share sa’o’i da yawa da bature, da kuma ganawa da baturiya a karo na farko. Suna kallonshi a gefen titi suna murmushi. Suka ce “GOOD LUCK”. Sai Dan Kasa ya hade fuska, yace “NO, DAN KASA”. Sai suka fashe da dariya. Baturiya tace “GOOD LUCK DAN KASA”. Sai ya girgiza kai yace “ME I NO BE GOODLUCK, JONATHAN YANA NAJERIYA, ME NAME SHINE DAN KASA OR KAMEEL USMAN CHAZALI. NOT GOODLUCK”. Har turawan zasu ja mota su tafi, sai suka tsaya. Baturen ya fito daga gaban mota, ya bude bayan mota ya dauko wata bakar jaka mai taya. Sai ya bude bayan mota, ya juye duka kayan dake cikin wanann jaka, wadanda yawancinsu kayan sawa ne da takalma da takardu. Bature ya mikawa Dan Kasa yace “TAKE, FREE”. Dan Kasa ya wangame baki da murna, yace “THANK YOU”. Bature yace “YOU ARE WELCOME”. Dan Kasa ya maimaita “YOU ARE WELCOME BATURE”. Sai Dan Kasa ya daga hannunsa na dama, yace “HIGH 5”. Bature ya wangame baki da murmushi, ya daga nashi hannun ya mayar masa. Bature ya shiga mota yana murmushi, suka yi gaba. Dan Kasa na tsaye da sabuwar jaka, ga Ghana-Must-Go a gefensa. A ranshi yace “YAU GA DAN KASA A TURAI”.

Domin sauraron sautin wannan labarin, a latsala nan https://radiyontalaka.com/2020/06/01/labarin-dan-kasa-a-turai-1/

A biyo mu a kashi na gaba domin jin cigaban wannan labarin. Mukhtar Jarmajo nayi shiru ba zan fallasa wa kowa cewa wannan labarin ka ne.

Dakta Bello Galadanchi

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.