Home / Big News / Yan Sanda Sun Kama Motar Kifi Dauke Da Mutane 91 A Kaduna

Yan Sanda Sun Kama Motar Kifi Dauke Da Mutane 91 A Kaduna

Kwamishinan Yan sandan Jihar Kaduna Umar Musa Muri, ya bayyana wa manema labarai cewa sun kama wata motar daukar Kifi dauke da Mutane 91, Awaki da Babura a babban titin garin kaduna na Yamma da ake cewa bypass.
Kwamishinan ya bayyana cewa sun kama direban motar mai suna Abdurrazak da ya shaida masu cewa motar ta taso ne daga Jihar Katsina kuma mallakar wani kamfanin kifi ne a Katsina kuma zai kai mutanen ne garin Legas.
Kamar yadda direban ya shaidawa manema labarai bayan da Jami’an yan sanda suka yi nasarar kama shi da motar ya ce daga Katsina ya taso kuma ya dauko mutanen ne a garin Zariya kuma zai kai su Legas, sai dai ya tabbatar da cewa ba shi ne ya yi wa motar Lodin ba.
Indai za a iya tunawa irin wannan tafiya zuwa garin Legas da za a hada tarin mutane da Dabbobi da kuma Baburan hawa daga arewacin Nijeriya ba sabon abu bane kasancewar wasu yan Arewa da yawa sun saba da hakan tsawon lokaci.
Saboda a wasu lokuta zaka ga mutanen da ke son zuwa Legas neman kudi ko garin Lokwaja sun Saba da hawan manyan motoci domin kawai neman sauki.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.