Daga Imrana Abdullahi
Jigo a jam’iyyar APC a Najeriya daga Jihar Katsina Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa lokaci ya yi da arewacin Najeriya za su sakama dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Hakika Bola Ahmed Tinubu ya taka rawar gani wurin kawo APC kan karagar mulki karkashin Mihammadu Buhari saboda haka lokaci ya yi da za a rama masa irin abin da ya yi.
Sanata Abu Ibrahim ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin APC ziyara a ofishinsa.
Ya kuma bayyana irin yadda Tinubu ya taimakawa Atiku Abubakar lokacin da ya yi takara karkashin jam’iyyar ACN da kuma yadda ya taimakawa Muhammadu Buhari shima ya zama shugaban kasa a APc.
Sanata Abu Ibrahim sai ya tabbatarwa duniya cewa Tinubu mutum ne da ke matukar Kaunar yan arewacin Najeriya baki daya,” saboda haka idan an zabe shi matsayin shugaban kasa zai kare mutunci da martabar arewacin Najeriya”.
“Zai yi wa kasa baki daya aiki, kuma yankin arewacin Najeriya ma zai amfana da irin kokarin ciyar da kasa gaba da aka san Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da shi, musamman kamar irin wanda ya yi a lokacin da yake matsayin Gwamnan Jihar Legas”.
Sai Sanata Abu Ibrahim ya shawarci jama’a da su tabbatar sun zabi APC da yan takararta tun daga dan takarar Gwamna Dokta Dikko Umar Radda, yan majalisun Jiha, Yan majalisar wakilai da yan majalisar Dattawa baki daya.
Ya bayyana dan takara Dikko da cewa “mutum ne mai dimbin basira, fikira da kirkirar abubuwan ci gaban jama’a da zai kai kowa ga nasara idan an zabe shi Gwannan Jihar Katsina”, inji Abu Ibrahim.
Ya kara da cewa ya zuwa yanzu na dawo Jihar Katsina domin in jagoranci batun tattaunawa da sasanci da kuma fadakar da jama’a irin nagartar Tinubu da Dikko, wandanda idan jama’a sun zabe su za a samu tabbataciyar nasara.
Sanata Abu Ibrahim ya ci gaba da cewa a halin yanzu ya na zagaya wa ko’ina ne a cikin Jihar Katsina da nufin ganin Bola Ahmed Tinubu da Dikko Umar Radda sun lashe zaben da ke zuwa.
A jawabinsa, dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin jam’iyyar APC Dokta Dikko Umar Radda godiya ya yi ga Abu Inrahim a matsayinsa na Uba da ke bashi shawarar duk irin abin da ya dace ayi.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa a matsayin Sanata Abu Ibrahim da ya kasance babban jigo a farfajiyar Yakin neman zaben Bola Tinubu, za a samu nasara cikin sauki idan zabe ya zo.
Da yake gabatar da nasa jawabin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina Alhaji Bala Abubakar Musawa cewa ya yi hakika irin yadda Sanata Abu Ibrahim ya tattara baki daya ya dawo Jihar Katsina sun tabbatar da samun nasarar lashe zaben Tinubu da Dikko ba tare da wata tantama ba.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC APC Abu ne da ke zaman tsintsiya madaurinki daya,”Mu duk daya ne don haka babu wani Rabe raben kawuna a cikin jam’iyyar”.