DAGA IMRANA ABDULLAHI
Umar Suleiman Kauran Wali, kuma dan takarar neman kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna ne a karkashin jam’iyyar Lebo, ya bayyana cewa lokacin yin siyasar bauta a karamar hukumar Kudan ya wuce.
Dan takara Umar Suleiman da aka fi Sani da Shatiman Kauran Wali, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Honarabul Umar Shatiman Kauran Wali, ya ci gaba da cewa a matsayinsa na mataki mai jini a jiki ya lashi Takobin ganin ya jagorancin matasa domin a fadakar da su illolin yin siyasar bauta da wasu masu son zuciya suka dade suna Jefa matasa a ciki.
Shatiman na Kauran Wali ya ci gaba da cewa zai tabbatar wa da al’ummar karamar hukumar Kudan da ke Jihar Kaduna sun samu ingantacce kuma Nagartaccen wakilci a majalisar dokokin Jihar Kaduna, sabanin irin abin da aka dade ana yi a ci gari da jama’a amma a barsu da kuturun Bawa saboda tsananin son zuciya kawai , muna fadakar da jama’a cewa su tabbatar sun bayar da cikakken hadin kai da dukkan goyon bayan da yakamata ga jam’iyyar Lebo sakamakon ita ce mai kyawawan kudirorin da za su kawo ma jama’a ci gaban da ya dace a kowa ne irin mataki musamman a matakin Karamar hukumar Kudan”.
Shatiman Kauran Wali ya kara da cewa tun a yanzu za a iya ganin cewa abin da jam’iyyar Lebo ta yi na salon kaddamar da masu yi mata Yakin neman zabe da yan takarar Gwamna da Mataimakinsa da kuma muhimman kudirorin da za ta aiwatar idan Allah ya ba su jagorancin Jihar Kaduna ba irin na sauran jam’iyyu bane sam sam, saboda haka Ko a nan farko ma akwai bambanci kwarai da gaske”.
“Kuma kasancewar jam’iyyar Lebo ta daya a jerin jam’iyyun Najeriya kasancewar PDP, APC da masu kayan Gwari duk jama’a sun Gaji da su musamman a karamar hukumar Kudan, kuma dalili na na yin wannan maganar ita ce jam’iyyar PDP ta yi mulki a tsawon Shekaru Goma sha Shida (16) APC kuma na shekaru kusan Takwas (8) sai kuma jam’iyyar NNPP jagoranta a karamar hukumar Kudan ya samu dama da yawa a can baya amma ba wani abu sai sabanin abin da jama’a ke bukata kawai aka gani, shi yasa nake tabbatar maka cewa jam’iyyar Lebo matasa suka runguma domin ita ce za ta share mana hawaye a karamar hukumar Kudan. Duba da irin jagoran da muke da shi a matakin kasa wato sakataren jam’iyyar Lebo na kasa da ya kasance dan asalin wannan karamar hukuma Honarabul Umar Ibrahim Mairakumi koda ya samu dama a baya ya taimaki mutane wanda tsohon shugaban karamar hukuma ne na karamar hukumar kudan ya yi amfani da damar ya gina al’umma sosai, domin ya Gina asibitoci, makarantu da sauran abubuwan da ake amfani da su da dama.
“Mun ga iyayen mu sun yi wa wasu Bauta a karamar hukumar nan kuma kamar yadda masu magana kan ce amfanin tuntubi romo, ko bauta lake yi ya dace ace kana da Lada, kakannin mu da iyayen mu sun yi wa PDP da APC bauta amma ba wata ribar da suka samu shi yasa nake gaya maku jam’iyyar Lebo ce ta daya a karamar hukumar Kudan. Mun karbi jama’a da dama sama da dubu Biyar da suka Baro jam’iyyun APC da PDP zuwa Jam’iyyar Lebo, kuma sunan mazabar da aka amshi mutanen nan tabon Sani mazabar Sakataren jam’iyyar Lebo na kasa, kuma a kowace mazaba akwai sunayen mutanen da suka dawo jam’iyyar Lebo za kuma mu zagaya ko’ina mu amshesu daki daki su samu damar bayar da ta su gudunmawar”. Inji Shatiman Kauran Wali.
Kamar da can a baya a karamar hukumar Kudan ” komai cancantarka komai iliminka idan kai ba dan koren Boka bane ta ba za a yi komai da kai ba domin ko an ajiye ka an san zaka matsa gaba domin ka taimaki na baya da kai, an kuma tsere mana wajen sama wa jama’a aikin yi misali idan ana daukar yan Sanda sai kaga sauran kananan hukumomi duk sun tsere mana a karamar hukumar Kudan sai kaga wasu ma da ba yan asalin wurin ba suna yin amfani da sunan karamar hukumar suna samun aiki duk da cewa dama ce ta karamar hukumar Kudan saboda haka a karkashin jagorancin da zan yi duk sai an gyara irin wadannan abubuwan”.
“Ni na fito ne daga mazabar Kauran Wali ta Arewa ne, ina sane kuma duk jama’a sun Sani cewa a mulkin APC na shekaru Takwas (8) ba wani abu da aka yi wa jama’a na aiki a mazabar Kauran Wali ta Arewa aikin da ya kai akalla na naira dubu dari, ba kuma Kauran Wali ba ne kadai duk mazabun da kaje ba komai. Haka duk wadanda suka samu dama a can baya a garuruwansu kawai suka tsaya duk wani abin da waninzai ce ya yi a PDP idan ka cire Kudan,Likoro da Hunkuyi nan ne kawai wani zai ce maka ga abin da aka yi a can baya fa kenan, don haka mu daga yankin Kudan ta Gabas idan mun samu dama za mu yi aiki ba tare da nuna wani bangaranci ba”, inji Umar Suleiman Shatiman Kauran Wali.