Home / Labarai / Majalisa Ta Nemi A Kammala Gyaran Hanyar Zariya Zuwa Fambeguwa

Majalisa Ta Nemi A Kammala Gyaran Hanyar Zariya Zuwa Fambeguwa

 

 

Daga Bashir Bello, Abuja

 

Majalisar Wakilan Nijeriya ta bukaci Ma’aikatar ayyuka da gidaje ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin kammala aikin gyaran hanyar da ta tashi daga Zariya zuwa Fambeguwa da ke jihar Kaduna, Arewa maso yammacin Nijeriya.

 

Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wani kudiri da Dan majalisar tarayya Mai wakilitar mazabar Ikara da Kubau ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.

 

Da yake gabatar da kudirin Honarabul  Hamisu Ibrahim ya bayyana cewa Ma’aikatar ayyuka da gidaje ta baiwa kamfanin “Proportion and Dredge Works Limited”  kwangilar gyara hanyar Zariya zuwa Pambeguwa a kan kudi Naira biliyan 10.1 a watan Mayun 2017 inda ake sa ran gamawa a watan Faburairun 2019.

 

Titin Zariya zuwa Pambeguwa mai Nisan Kilimita 88.4 ya ratsa birane da kauyuka da Kuma Gonaki a cikin kananan hukumomi biyar da suka hada da Zariya, Soba, Kubau, Kauru da Lere wadanda galibinsu manoma ne da ke bada gudunmawa Kashi 75 cikin 100 na masarar da ake samarwa a Jihar Kaduna.

 

Har ila yau Honarabul Hamisu ya ce rahotanni sun yi nuni da cewa kawo yanzu Kanfanin da ke aikin kwangilar ya kammala Kashi 13 cikin 100 na aikin ne kadai, sakamakon tsaiko da rashin sanin makamar aiki.

 

Ya ce abin takaici ne yadda hanyar ta lalace sakamakon tsaikon da ake ci gaba da samu wajen kammala aikin da Kuma muggan ramukan da ke titin, wanda hakan ke nuna cewa kamfanin ba zai iya yin aikin ba.

 

Ya kara da cewa mummunan halin da hanyar ke ciki ya yi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyoyi yayin da Kuma ta kasance mai mummunan hadari.

 

Daga karshe majalisar ta bukaci Ma’aikatar ayyuka da gidaje ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin kammala aikin hanyar,
Yayin da ta dorawa kwamitin ayyuka alhakin tabbatar da wannan umarni.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.