Kamfanin matatar Mai ta Alhaji Aliko Dangote, ya bayanna rage farashin litar Mai ga Yan Kasuwar zuwa naira 970.
Babban Jami’in sadarwa na kamfanin Anthony Chiejina, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda ya ce a daidai lokacin da aka shiga karshen Shekara ya dauki wannan mataki domin nuna goyon baya ga alummar najeriya ta yadda abinda suke zato zai tabbata.
Ya ce kamfanin ba zai yi Kasa a gwaiwa ba wajen daukan irin wannan mataki ta hanyar samar da ingantaccen Mai.
Ya tabbatar da cewar Kamfanin na yin dukkanin maiyiyuwa domin biyan bukatun al’ummar Najeriya ba tare da nuna gajiyawa ba na samar da man fetur Mai Inganci ga Najeriya.