Home / Labarai / MASARI AYI HATTARA DA AIKIN RAJISTAR ZABE A JIHAR KATSINA – MELA MASKA

MASARI AYI HATTARA DA AIKIN RAJISTAR ZABE A JIHAR KATSINA – MELA MASKA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Wani jigon al’umma a Jihar Katsina Alhaji Rabi’u Lawal Maska da ake kira “Rabe Mela” ya yi kira ga hukumar zabe da sauran masu ruwa da tsaki a fadin tarayyar Najeriya musamman Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari da su mayar da hankali game da irin yadda ake aikin rajistar jama’a domin gujewa yi wa jama’a sakiyar da ba ruwa.

Alhaji Rabi’u Lawal Maska ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa ta wayar salula da wakilinmu.
Alhaji Rabi’u Mela Maska ya ci gaba da cewa ya na yin wannan kokarin fadakarwa ne domin ya kara ankarar da Gwamnan Jihar Katsina kada a yi sake a yi wa jama’ar kasa sakiyar da ba ruwa kasancewar dimbin jama’a ba su da wata masaniyar yin amfani da na’ura mai kwakwalwa kuma a halin yanzu ana amfani da tsarin na’ura mai kwakwalwa ne wajen yi wa jama’ar kasa rajistar da za su yi zabe nan gaba”.
Ya kara da cewa kasancewar jama’a ba su da ilimin yin amfani mai kwakwalwa kuma kusan wuraren da al’ummar karkara ke zaune wurare ne da babu yanar Gizo don haka ya dace ayi hattara kwarai wajen aiwatar da wannan aikin.
“Ni a matsayi na dan Jihar Katsina mai kishin ganin ci gaban jama’a koda yaushe nake fadakar wa ga Gwamnati da sauran al’umma baki daya kuma musamman Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da ya mayar da hankalinsa a kan batun yi wa jama’a rajistar da za a yi zabe da ita da a halin yanzu ake yin ta a hanyar amfani da yanar Gizo”, inji Mela Maska.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.