Home / Kasuwanci / Kamfanoni Sama Da 90 Sun Halarci Taron Baje Kolin SMEDAN A Kaduna

Kamfanoni Sama Da 90 Sun Halarci Taron Baje Kolin SMEDAN A Kaduna

Kamfanoni Sama Da 90 Sun Halarci Taron Baje Kolin SMEDAN A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin Gwamnati na ganin ta wayar da kawunan masu kanana da matsakaitan masana’antu a Jihar Kaduna a halin yanzu aka shiryawa yan kungiyoyi masu sana’o’i da kuma kamfanoni domin karin fadakarwa da kuma bayar da Tallafi ga mahalarta baje kolin.
Kamar yadda muka samu labari taron baje kolin ya samu halartar a kalla mahalarta daga kamfanoni da kungiyoyin sana’o’i guda 90 da a halin yanzu an raba masu abinci kyauta da wurin zama kyauta, kuma ana saran za a bude taron a gobe Juma’a domin kara zaburar da masu kananan kasuwanci.
Wannan taron kungiyoyin sana’a da kamfanonin kanana an shirya shi ne tare da hadin Gwiwar ma’aikatar kasuwanci da kirkire kirkire ta Jihar Kaduna da kuma hukumar SMEDAN.
Kamar dai yadda muka samu bayanai sun tabbatar mana cewa a kalla mutane Tamanin (80) ne aka shirya za a dauki nauyin domin baje kolin, amma a halin yanzu mahalarta taron sun kai Casa’in da suka halarci filin kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna.
An saran shugaban hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu ta kasa ( SMEDAN) Honarabul Dokta Dikko Umar Radda zai bude baje kolin a Kaduna.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.