Home / Labarai / Masari Ya Amince Da Ma’aikata Su Koma Aiki A Jihar Katsina

Masari Ya Amince Da Ma’aikata Su Koma Aiki A Jihar Katsina

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji  Aminu Bello Masari, ya amince da batun komawar ma’aikata wuraren ayyukansu a matakin Jiha da kananan hukumomin Jihar baki daya, saga ranar Litinin mai zuwa 8 ga wannan watan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar da ta fito daga ofishin babban sakatare mai kula da harkokin mulki a ofishin shugaban ma’aikata Alhaji Lawal Ado Dutsinma, inda ya bayyana cewa aka bayyana cewa an dage dukkan wata doka da kuma hana zirga zirga a karkashin dokar rufe wurare a Jihar katsina.
Takardar da bayar da umarni ga dukkan manyan Sakatarori da shugabannin bangarorin Gwamnati da su tabbatar da ma’aikata sun koma aiki kamar yadda dokar aikin ta tsara.
Kamar yadda takardar ta bayyana cewa tanaje tanajen sun hada da ajiye abubuwan wanke hannu da ma’aikatu da hukumomin Gwamnati.
Takardar ta ci gaba da cewa a tabbatar ma’aikata sun yi amfani da Takunkumin rufe baki da hanci a wuraren ayyuka kuma a tilasta samar da tazara a Ofisoshi da wuraren aiki.
Takardar ta bukaci manyan sakatarorin da shugabannin hukumomin Gwamnati da su tabbatar kowane ma’aikaci ya san an koma aiki domin yin biyayya ga umarnin.

About andiya

Check Also

NTI in Collaboration with UNESCO TRAINS 250 Teachers on HIV Education, Family Life

By; Imrana Abdullahi The Director and Chief Executive of NTI, Prof. Musa Garba Maitafsir said …

Leave a Reply

Your email address will not be published.