Home / MUKALA / Dokta Garba Dantutture ya yi tuntubbe

Dokta Garba Dantutture ya yi tuntubbe

A ‘yan kwanakin nan wasu faya-fayan bayanai da Dokta Garba Isiyaku Dantuture, Magatakardan Kwalejin Horas da Mallamai ta Tarayya (FCE) Katsina ya yi akan harkokun siyasa ya ke ta yawo a kafafen watsa labari na zamani.
Kalaman da Dokta Garba Isiyaku ya yi sun biyo bayan wani taron karramawar da wasu matasan yankin Gundumar Danejin Katsina, Hakimin Mahuta da ke Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina suka yi masa. An shirya karramawar ne, a cewarsa, domin nuna jin dadin kwazon da Dokta Garba ya yi wajen samar da ayyuka ga wasu matasan yankin.
 Taron ya gudan ba tare da wata hatsaniya ba. Sai dai bayanan da suka fito daga bakin Dokta Garba sun nuna cewa akwai wata manufa da shirin ya kunsa dangane da harkokin siyasa yankin. Da farko ya shirya shimfida salon siyasar tashin hankali wadanda zai iya jawo salwantar rayukan jama’a da barnar dukiyoyi ba gaira ba sabas.
A cikin bayanan Dokta Garba ya nuna yadda ya tanadi kimanin matasa 200, ya ba su kayan maye, musamman tabar wiwi da makamai da suka hada da adduna da takubba da gorori domin kawar da wanda ko wadanda suka shiga tsakaninsu da manufofi su. Wanan batu da ya yi ya sabawa maganarsa ta farko, cewa matasan su ne suka shirya taron.
Daga cikin burinsa akwai canza salon siyasar yankin ta hanyar juyin juya hali, yana mai cewa kallon kashi ya ke yi wa ‘yan siyasar yankin tare da shan alwashi sai ya ga bayansu. Daga cikin mutanen da ya ke yi wa kallon kashi akwai Alhaji Aminu Bello Masari, Gwamna Jihar Katsina da shakikinsa, irin su Alhaji Bello Kagara, darakta a Hukumar UBEC da Hon Kabir Barau Dankanjiba, da Hon Ibrahim Mahuta Dan majalisa tarayya mai wakiltar Malumfashi da Kafur da Hon. Abubakar Husaini Dankanjiba mai wakiltar Karamar Hukumar Kafur a Majalisa Dokokin Jihar Katsina.
Dokta Garba ya ce ya koyi yadda ake neman mulki ta hanyar amfani da salon juyin juya hali ne daga maigidansa Sanata Danjuma Goje, tsohon gwamna Jihar Gombe wanda sai da kimanin mutane 100 suka rasa rayukansu kafin ya zauna daram kan kujerar sa ta Gwamnan Gombe. Ya ce muddin ana son a samu canji a salon siyasar yankin sai an yi amfani da wannan salo.
Babu shaka wanan babar Maganace mai muni musamman ga baban mutum irin wanan wada ana ganin yana chikin manyan jagororin Najeria, ba ma kamar Arewa.
Fitar wa’annan bayanai ta jawo ka ce na ce a rukunnan jama’a daban daban.
Akwai masu ganin cewa Dokta Garba Isiyaku ya yi kuskure domin shi ma’aikaci ne wanda ya kamata ya tsare aikinsa tare da bayar da gudunmuwarsa wajen kawo ci gaba ga jama’arsa, musamman ganin mukaminsa ba na siyasa ba ne.
Haka kuma akwai masu ganin cewa ya kamata Dokta Garba ya nemi hadin kan ‘ yan siyasa da ma’abota ilimi da sarakuna da shugabannin addini da shugannin kungiyoyin matsa domin fito da tsarin da zai amfanar da juma’a.
Mutane irin su Gwamna Aminu Bello Masari da Alhaji Bello Kagara da Hon Kabir Barau Dankanjiba sun kwashe fiye da shekara 30 akan farfajiyar siyasar wancan yanki da karamar hukuma da jihar Katsina da kuma Najeria baki daya. Hasali ma su ne kashin bayan kirkiro Karamar Hukumar Kafur da assasa ta. Wadannan mutane sun samu nasara a shimfida tsarin siyasa da ba a amfani da rikici da tashe-tashen hankula da suke jawo salwantar rayukan jama’a da dukiyoyi duk da cewa akan samu banvancin ra’ayi.
Haka kuma akwai masu ganin cewa dora matasa akan turbar siyasar ta’addanci yana da mummuna hadari ga kowace al’umma bama kamar idan aka yi dubi da irin mawuyacin halin tsaron da kasarnan take chiki.  Daya daga cikin manya matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a Nijeriya a halin yanzu suna da alaka da yadda miyagun ‘yan siyasa suka yi amfani da matasa wajen kaiwa ga madafan iko kuma su yi watsi da su bayan sun samu biyan bukata. Irin wadannan matasa ne suka koma ‘yan’taada masu kama mutane suna garkuwa da su, wasu kuma su koma ‘yan ina-da-kisa.
Haka kuma ganin irin halin da Jihar Katsina ke ciki dangane da rashin tsaro ba daidai ba ne wani ya cusa wa wasu matasa akidar siyasar tashin hankali da kashe jama’a.
Sanan wasuma na ganin kagene akayi wa Dakta Dantutture. Wanan ra’ayine na wadanda basu sami damar sauraren hakikanin kalamansi ba. Amma bisa ga dukkan alamu Dokta Garba Isiyaku Dantutture yana kokarin jawo matasa a jikin sa domin ya yi amfani da su ya cimma wani burinsa na siyasa.
Akwai masu ganin ya kamata hukuma ta duba wannan al’amari cikin hanzari don tsamo matasan da Dokta Garba Isiyaku Dantuture ya tanada domin kawar da su daga wancan mugun  tsari da aka dora su a kansa.
Mohammad Lawal Mai kudi ne ya rubuta mukalar domin amfanin jama’a.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.