Home / Labarai / Masari Ya Bada Umarnin Ci gaba Da Yin Sallar Juma’a

Masari Ya Bada Umarnin Ci gaba Da Yin Sallar Juma’a

 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Katsina ta sassauta dokar hana zuwa Sallar Juma’a wadda za’a cigaba daga wannan satin akan wasu tsare-tsare da dokoki da tayi kamar haka:
1. Bada dama ga wasu Manyan Masallatai tare da samar masu abubuwan kariya irinsu: i. Tankunan ruwa ii. Sabullai iii. Abin kariyar hanci da baki (face mask)
2. Takaita Hudubobi da Sallah domin sallamar al’uma cikin lokaci
3. An bada dama ga duk wani Masallacin Juma’a yin Sallah matukar zai tanaji duk irin abubuwan da Gwamnati ta tanada a Masallatan da taba damar yin Sallar.
Muna rokon Allah ya kara tsaremu daga wannan annoba inda kuma ta shiga Allah ya yaye masu ita.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.