Home / Labarai / WASU MUTANEN MASARI SUN BARKE DA KUKA A KATSINA

WASU MUTANEN MASARI SUN BARKE DA KUKA A KATSINA

 

….Ya ce Kwamishinoni, Masu Bashi Shawara, ” Mun yi Bakin Kokatin mu”.

 

Daga Imrana Abdullahi

 

 

Ya kasance wani wurin da ake ta barke wa da kuka a ranar Laraba da maraice a cikin gidan Gwannatin Jihar Katsina yayin da Gwannan Jihar Aminu Bello Masari ya kasa rike hawayen da suke fita masa a idanunsa lokacin da yake yi wa mambobin majalisar zartaswar Jihar jawabi a wani babban taron da suka yi gabanin Rantsar Rantsar sabuwar Gwamnatin jihar a ranar 29 ga watan Mayu.

Haka nan shima mai bayar da shawara ga jam’iyyar APC a kan harkokin shari’a Ahmad Usman El- Marzuk, da ya kasance mai shari’a na Jihar duk shima ya barke da kuka a lokacin da yake nasa jawabinsa.

A tsakiyar taron, abin da ba asaba gani ba Masari ya bar ainihin dakin taron ne ba tare da shiri ba sakamakon irin yadda kukan ya ki tsayawa.

Tun da farko Masari a cikin jawabinsa “A cikin watan Yuni na shekarar 2015, mun Sani cewa wata rana za mu bar mulkin saboda haka lokaci yazo yanzu lokacin barin Gwannatin ya yi saboda wannan shi ne taron majalisar zartaswar mu na karshe tare da Masari a matsayin Gwamna.

“Wannan ba shi ne karshen tashin duniya ba kuma ba shi ne karshen rayuwar mu ba”.

“Ba mu dauki duk wani mataki ba saboda biyan bukata na kashin kan mu ba ko domin son zuciya, ko domin mu cutar da wani ko wasu ba ko domin mu kare ko hana wani ya samu wata damamu kuma yi iyakar bakin kokarin mu da zamu iya yi”.

Sai ya godewa mambobin majalisar zartaswar bisa irin kokarinsu da jajircewarsu musamman a wajen ganin an cimma nasara.

Masari ya shawarci jama’a da su tabbatar da bayar da hadin kai da goyon bayansu ga Gwannati mai zuwa karkashin Dokta Dikko Radda.

Ya ce duk da wadansu tarnaki da wahalhalu, amma suk kowa ya dage a cikin Gwannatin nan har aka samu nasarar da aka samu cimma wa a tsawon shekaru Takwas don haka muke cewa wadannan mutane sun yi iyakar bakin kokarinsu”.

“A tsawon shekaru Takwas da muka yi muna tare, mum to iyakar bakin kokarin mu”, inji Masari

“Mai girma Gwamna ka wuce shugaba kawai a gare ni “, El- Marzuk ya gayawa Gwamna a cikin jawabinsa.

Kamar yadda ya ce ” Ka zamo Iba mai yi mana nunin hanya ta alkairi, dan USA la nuna Mani jin tausayi, taimako da kuma girmamawa tare da taimakawa a koda yaushe.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.